Tinubu Ya Shiga Taron FEC Ana Rade Raɗin Za a Kori Wasu Ministoci, Bayanai Sun Fito
- Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa FEC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ana tsaka da raɗe-raɗen zai kori wasu ministoci
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya yabawa Tinubu bisa nasarar da APC ta samu a zaben jihar Edo kafin fara taron
- Majiyoyi da dama sun yi iƙirarin cewa nan ba da daɗewa ba Shugaba Tinubu zai yi garambawul a majalisar zartaswa da ministoci suke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartaswa (FEC) yanzu haka a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
Wannan taro na zuwa ne a daidai lokacin da bayanai daga ɓangarori da dama ke nuna cewa shugaban ƙasar na dab da yin garambawul a gwamnatinsa.
Tinubu, wanda ya sha alwashin korar duk ministan da ya zama ɗan dumama kujera, ya yi gum da bakinsa game da batun garambawul a majalisar zartaswa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akume ya yabawa Bola Tinubu
Daily Trust ta tattaro cewa gabanin fara taron FEC yau, sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya yabawa Shugaba Tinubu kan kokarinsa na inganta damokuraɗiyya.
Sanata Akume ya jinjinawa shugaban ƙasa ne bisa yadda aka gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar Edo ranar Asabar da ta gabata.
Akume ya kuma yabawa shugabannin jam’iyyar APC na jihar Edo waɗanda suka jagoranci nasarar Sanata Monday Okpebolo.
FEC ta yi jimamin rasuwar tsohuwar minista
Bugu da ƙari sakataren gwamnatin ya tunawa ƴan majalisar rasuwar tsohuwar ministar harkokin mata da ci gaban matasa, Misis Salome Jankada rasuwa.
Misis Salome Jankada ta kasance ministar harkokin mata da ci gaban matasa a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Wannan dalili ne ya sa FEC ta yi shiru na minti ɗaya domin karrama marigayyar da ta rasu ranar 27 ga watan Agusta, 2027.
Mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da kusan dukkan ministoci sun halarci taron na yau Litinin, 23 ga watan Satumba, 2024, rahoton Punch.
"Aiki na zo yi" - Tinubu
A wani rahoton kuma shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan dalilin zuwansa fadar shugaban kasar Najeriya domin cirewa mutane shakku.
Bola Ahmed Tinubu ya ce aiki ne ya kawo shi fadar shugaban kasa ba wai neman kudi da amfani da damar ta wata hanya daban ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng