Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ajiye Aiki karkashin Tinubu? Bayanai Sun Fito

Shugaban Sojojin Najeriya Ya Ajiye Aiki karkashin Tinubu? Bayanai Sun Fito

  • Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa kan raɗe radin da ke nuni da cewa Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya mika takardar ajiye aiki
  • Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya yi karin haske kan maganar ajiye aikin
  • A makon da ya wuce ne wasu kafafen sadarwa suka wallafa cewa Laftanal Janar Taoreed ya ajiye aiki saboda barazana da aka masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta yi karin haske kan raɗe radin cewa shugabanta, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ajiye aiki.

An yaɗa raɗe radin cewa Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya riga ya tura takardar ajiye aiki ga shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Zulum ya fadi jaruman da suka rage aukuwar asarar rayuka

Sojojin Najeriya
Sojoji sun karyata cewa shugabansu ya ajiye aiki. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta tuntubi Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu domin yi mata karin haske.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar ajiye aikin shugaban sojoji

Wasu kafafen sadarwa a yanar gizo sun wallafa cewa shugaban sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ajiye aiki.

Kafafen sun ce lamarin ya faru ne sa'o'i 24 bayan Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya tsallake rijiya ta baya a wani yunkurin kashe shi da aka so yi.

Haka zalika kafafen suka ce wai ajiye aikin Laftanal Janar Taoreed ta jefa rundunar sojin Najeriya cikin ruɗani a wannan lokacin.

Da gaske shugaban sojoji ya ajiye aiki?

Daraktan yada labaran rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya ce sam ba gaskiya kan cewa shugaban sojoji ya ajiye aiki.

Saboda haka Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya yi kira ga yan Najeriya kan su yi watsi da labarin domin ba shi da tushe kwata kwata.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya yi bayani kan karbar tuban Bello Turji da sauran yan bindiga

Tun a ranar 19 ga watan Yulin shekarar 2023 ne dai shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Laftanal Janar Taoreed Lagbaja shugaban sojojin Najeriya.

An lakadawa soja duka a Oyo

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa wasu matasa a jihar Oyo sun lakaɗawa wani sojan Najeriya duka bisa zargin kisan kai.

Matasan sun zargi sojan ne da harbe wani jami'in NSCDC mai suna Olapade Segun a wani waje a yankin Bodija a jihar Oyo bayan sun yi rigima.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng