Fargabar Barkewar Rikici a Edo: 'Yan Sanda Sun Dauki Matakai bayan Nasarar APC
- Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce ta dauki matakai na dakile duk wata baranzana da za ta kawo cikas ga zaman lafiya a Edo
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman dari dari a Edo tun bayan da hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaben jihar
- Kakakin ‘yan sandan na kasa, Olumuyiwa Adejobi ya ce an tura karin jami'an tsaro zuwa cibiyoyin INEC da manyan kadarorin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Ana ci gaba da zaman dari dari da fargaba a Edo tun bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta fadi wanda ya lashe zaben jihar da aka gudanar.
Rundunar 'yan sanda ta tura karin jami'anta zuwa cibiyoyin INEC, manyan kadarorin gwamnati da mutanen da suka taka rawa a zaben jihar na ranar Asabar.
Kamar yadda rahoton jaridar Premium Times ya nuna, rundunar ta dauki wannan mataki ne domin dakile duk wani rikici da ka iya barkewa a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yanayin tsaro kafin zaben Edo
Kakakin ‘yan sandan na kasa, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
A ranar Lahadi ne hukumar zaben ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebolo a matsayin wanda ya lashe zaben.
Kafin zaben dai an samu tashin hankali a jihar Edo, lamarin da ya sa aka baza jami'an tsaro da dama a jihar. 'Yan sanda sun jibge jami'ansu 35,000 a fadin Edo.
Yanayin tsaro bayan kammala zabe
An ruwaito cewa wasu magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar sun mamaye hedikwatar INEC suna zanga-zangar adawa da sakamakon da hukumar ta fitar.
Mista Adejobi ya ce yayin da aka kammala zaben, mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (DIG) mai kula da zaben, Frank Mba ya dauki matakan tsaro na bayan zabe
Ya ce an dauki wannan matakin ne domin tabbatar da cewa a shirye rundunar ta ke na mayar da martani ga duk wata barazana da za ta iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar.
APC ta lashe kananan hukumomi 11 a Edo
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar APC da dan takararta, Monday Okpebholo sun lashe zaben gwamnan jihar Edo, inda suka samu nasara a kananan hukumomi 11.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa Monday Okpebholo ya samu jimillar kuri'u 291,667 yayin da Asu Ighodalo na PDP ya samu kuri'u 247,655.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng