Matasan N Power Sun Nuna Damuwa, Sun Aika Sako ga Shugaba Tinubu

Matasan N Power Sun Nuna Damuwa, Sun Aika Sako ga Shugaba Tinubu

  • Matasa ƴan N-Power sun nuna damuwa da shirin gwamnatin tarayya na rusa ma'aikatar harkokin jin kai da yaƙi da fatara
  • Shugaban N-Power na jihar Kano, Nazifi Mohammed Abubakar ya ce ma'aikatar ce kaɗai wata hukumar gwamnati mai alaka da talakawa
  • Nazifi ya buƙaci gwamnati ta sake nazari kan shirinta, maimakon haka ta ƙarawa ma'aikatar ƙarfi domin magance ƙuncin da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Matasa masu cin gajiyar shirin N-Power sun yi Allah wadai da shirin da gwamnatin tarayya ke yi na rusa ma’aikatar jin kai da yaki da fatara.

Shugaban ƴan N-Power reshen jihar Kano, Nazifi Mohammed Abubakar ya nuna damuwa matuƙa da jin labarin shirin gwamnati na rusa ma'aikatar jin ƙai.

Kara karanta wannan

Karkatar da tallafi: Ɗan majalisa ya fusata, ya shirya maka gwamna a gaban kotu

Shugaba Tinubu da masu cin gajiyar N-Power.
Masu cin gajiyar N-Power sun yi watsi da shirin rushe ma'aikatar jin kai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, N-Power
Asali: UGC

Nazifi ya bayyana rawar da ma'aikatar ke takawa wajen ayyukan jin ƙai, rage talauci da kuma walwala da jin daɗin ƴan Najeriya, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan N-Power sun nuna damuwa

A cewarsa, kafa ma’aikatar wani shiri ne mai kyau da ake buƙata wajen gudanar ayyukan jin kai, magance bala’o'i, da kuma shirye-shiryen jin dadin jama’a a kasar nan.

Ya ce soke ma'aikatar zai kawo cikas ga kokarin gwamnatin tarayya na magance kalubalen zamantakewa da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi.

Nazifi ya kara da cewa ma’aikatar jin ƙai ita ce kadai hukumar gwamnati da za ta iya aiwatar da kyawawan manufofin Shugaba Bola Tinubu, duba da kusancinta da talakawan Najeriya.

Masu cin gajiyar N-Power sun faɗi mafita

Ya ce ma’aikatar tana kula da shirye-shiryen masu ma'ana da suka hada da shirin N-Power, shirin tallafin kuɗi na CCT, da ciyar da ɗaliban makarantun firamare.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban NESG ya faɗi kuskuren Tinubu da ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala

Vanguard ta rahoto Nazifi na cewa:

"Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta sake nazari kan shirinta, maimakon haka ta karfafa kokarin ma’aikatar wajen magance wahalhalu da matsin tattalin arziki."

Wani ɗan N-Power a jihar Katsina, Abdullahi Tukur ya shaidawa Legit Hausa cewa idan wannan maganar ta tabbata, to lallai gwamnati mai ci ba talakawa ne a gabanta ba.

A cewarsa, duk da kura-kuran da aka tafka tun da aka kafa ma'aikatar a 2019, tana da muhimmanci wajen saukaƙawa al'umma musamman a halin da ake ciki.

Abdullahi ya ce:

"Rusa ma'aikatar jin kai ba shi ne mafita daga almundahanar da ake samu a cikinta ba, a magana ta gaskiya ma'aikatar tana taimakawa waɗanda ba su san kowa ba.
"Ka san Najeriya wa ka sani ne to amma a ma'aikatar baka san kowa ba zaka samu jarin sana'a idan kana da tattali. Batun N-Power kuma ni na riga na cire rai.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Gwamna ya gano mugun shirin da ƴan daba ke yi ana dab da fara zaɓe

"Bana ganin wannan gwamnatin za ta biya mu haƙƙinmu, domin alamu sun nuna ko kaɗan ba damuwar mu ce a gabansu ba, Allah ya kawo maka sauƙin halin da ake ciki."

N-Power: Tinubu ya kafa kwamitin bincike

A wani rahoton kuma bayan dakatar da ayyukan N-Power da duk wata hukumar tallafa wa jama’a, Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti.

Tinubu ya dauki matakin ne don tabbatar da bincike kan zargin badakalar da ta dabaibaye ma’aikatar jin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262