Zaben Edo: 'Yan Sanda Sun Yi Gargadi ana Dab da Fara Kada Kuri'a

Zaben Edo: 'Yan Sanda Sun Yi Gargadi ana Dab da Fara Kada Kuri'a

  • Al'ummar jihar Edo za su fito domin zaɓar gwamnan da zai jagorance su a ranar Asabar, 21 ga watan Satumban 2024
  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta buƙaci jama'a da su koma gidajensu bayan sun fito sun kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓen
  • Rundunar ƴan sandan ta bayyana cewa mutanen da ke da iznin kai da kawowa ne kaɗai za a ba damar yin zirga-zirga a lokacin zaɓen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta yi magana kan zaɓen gwamnan jihar Edo na ranar Asabar, 21 ga watan Satumba.

Rundunar ƴan sandan ta shawarci masu kaɗa ƙuri’a da su koma gida bayan sun kaɗa ƙuri'unsu.

'Yan sanda sun magantu kan zaben Edo
'Yan sanda sun bukaci mutane su koma gida bayan kada kuri'a Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wane gargaɗi ƴan sanda suka yi?

Kara karanta wannan

"Akwai matsala": Gwamna ya gano mugun shirin da ƴan daba ke yi ana dab da fara zaɓe

Mataimakin Sufeto Janar na ƴan sanda, Frank Mba, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Frank Mba ya bayyana cewa waɗanda kawai aka tantance domin kai da kawowa ne kaɗai za a ba damar yin hakan a lokacin zaɓen.

"Yana da muhimmanci iyaye da kowa su sani cewa idan ba a tantance ku domin yin wani aiki da ya shafi zaɓen ba, bai kamata ku fito kan titi ba."
"Ku fito kawai, ku je rumfar zaɓe, ku sauke nauyin da ke kanku na kaɗa ƙuri'a sannan ku koma gidajenku."

- DIG Frank Mba

Shirin ƴan sanda kan zaɓen Edo

Dangane da shirye-shiryen da ƴan sanda suka yi kan zaɓen, DIG Mba ya ce ƴan sanda sun tanadi komai domin gudanar da zaɓen na jihar Edo yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Babban hafsan tsaro ya yi gargadi yayin da ake shirin fara kada kuri'a

Zan iya cewa mun shirya komai, mun tura jami'an mu kuma mun magance dukkanin wasu matsaloli. Mun kula da hedkwatar INEC da cibiyoyin RAC. Saboda haka a shirye muke."

- DIG Frank Mba

Gwamna Obaseki ya yi fallasa

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo karƙashin jagorancin Gwamna Godwin Obaseki ta tono wata maƙarƙashiya.

Gwamnatin Obaseki ta ce ta gano cewa an ɗauko ƴan daba kuma suna nan suna shirin hargitsa ofisoshin hukumar zaɓe INEC a wasu kananan hukumomin Edo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng