Maiduguri: Gwamna Ya Dura Borno, Ya Ƙara Jiƙa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa da Miliyoyi
- Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya jagoranci tawagar gwamnatinsa da sarakuna sun kai ziyarar jaje Maiduguri a Borno
- A madadin gwamnatin Neja, Bago ya miƙa N250m ga gwamna domin a tallafawa waɗanda mummunar ambaliyar ta rutsa da su
- Gwamna Babagana Zulum ya yaba da karamcin Bago tare da yi masa alƙawarin cewa sakon zai isa ga waɗanda aka bayar dominsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Borno - Gwamnatin jihar Neja ta bayar da gudunmuwar kudi Naira miliyan 250 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Gwamna Umaru Bago ne da kansa ya jagoranci tawaga zuwa Maiduguri domin jajantawa gwamnati da al'ummar jihar Borno dangane da ambaliyar ruwan da ta afku.
Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin tada hankali da damuwa, wanda ke bukatar goyon baya da agaji daga dukkan ‘yan Najeriya, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bago ya jajantawa Maiduguri
Gwamnan ya karfafawa takwaransa na Borno, Farfesa Babagana Zulum da al’ummar jihar gwiwa kan su ƙara yin imani da Allah SWT wanda ba ya kuskure.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar Borno da su marawa Gwamna Zulum baya a kokarinsa na ganin rayuwarsu ta dawo daidai kamar da.
Gwamna Bago ya ƙara da cewa gwamnatinsa a shirye take ta tura malaman lafiya domin bayar da agaji idan buƙatar hakan ta taso.
Gwamna Zulum ya yabawa ƙoƙarin Bago
A nasa jawabin, Zulum ya gode da karamcin gwamnatin Neja, inda ya ba da tabbacin cewa za a yi amfani da kudaden cikin adalci wajen tallafawa wadanda ambaliyar ta shafa.
Farfesa Zulum ya yaɓa da salon mulkin Gwamna Bago da ci gaban da ya kawo Neja, inda ya ƙara da cewa gwamnan ya inganta dangantakar jihohin biyu.
Sakataren gwamnatin Neja, Abubakar Usman, hadimai, shugabannin kananan hukumomi, sarakunan Borgu da Kagara na cikin tawagar gwamnatin jihar Neja.
Tawagar jihar Neja ta kuma ziyarci fadar Shehun Borno domin jajanta masa kan wannan ibtila'i da kuma neman albarkar sarki, rahoton Punch.
Gwamna Zulum ya jinjinawa sojoji
A wani rahoton kuma gwamnatin Borno ta jinjina wa dakarun sojojin kasar nan kan yadda su ka taimaka masu da ambaliyar da ta girgiza babban birnin jihar
Farfesa Babagana Umara Zulum ne ya mika godiyar yayin da ya karbi bakuncin babban hafsan sojan kasar nan, Janar Chistopher Musa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng