Awanni Kadan kafin Zaben Edo, Rundunar Yan Sanda Ta Bayar da Umarni a Jiha

Awanni Kadan kafin Zaben Edo, Rundunar Yan Sanda Ta Bayar da Umarni a Jiha

  • Rundunar yan sandan kasar nan ta umarci a takaita da zirga zirga a ranar zabe da zai gudana ranar Asabar a Edo
  • Babban Sufeton yan sandan kasar nan, Kayode Egetokun ya bayar da umarnin a wani mataki na tabbatar da tsaro
  • Babban Sufeton ya bayyana cewa akwai wasu jami'ai da dokar nan ba ta shafe su ba saboda muhimmancinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Babban Sufeton yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin takaita zirga-zirga a jihar Edo yayin da ake shirin zabe a ranar Asabar.

An tsagaita zirga-zirga a tituna da hanyoyin ruwa daga 6.00 n.s zuwa 6.00 n.y a ranar Asabar da za a gudanar da zaben.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya tsawatarwa 'yan siyasa ana saura awanni a yi zaben Edo

Police
An takaita zirga zirga a Edo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an dauki matakin ne domin tabbatar an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali da lumana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaben Edo: Yan sanda sun tsagaita zirga zirga

Jaridar Punch ta wallafa cewa an dakatar da jama'ar gari daga zizrga-zirga daga safiya zuwa maraice yayin da ake tunkarar zaben Edo.

Babban Sufeton yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya ce wadanda ba dokar ba ta shafa ba sun hada da yan jarida da aka tantance, jami'an lafiya da jami'an zabe.

Yan sanda sun shirya wa zaben Edo

Rundunar yan sandan kasar nan ta haramta wa jami'anta raka yan siyasa da sauran muhimman mutane zuwa rumfunan zabe da wurin tattara sakamakon zabe.

Haka kuma an haramta amfani da jiniya a motocin da aka haramta duk a kokarin ganin an gudanar da zaben a cikin lumana.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Yiaga Africa ta lissafa garuruwa 8 da ka iya fuskantar tashin hankula

Zaben Edo: Tinubu ya yi gargadi

A baya kun samu rahoton cewa Bola Ahmed Tinubu ya shawarci yan siyasa da magoya bayansu su guji aikata duk abin da zai jawo tashe-tashen hankula a zaben Edo mai zuwa.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa akwai yakinin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa za ta gudanar da zabe cikin adalci, saboda haka a bar kowa ya zabi abin da ya ke so a ranar Asabar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.