SSCE 2024: Hukumar NECO Ta Fadi Adadin Makarantu da Suka Yi Satar Amsa

SSCE 2024: Hukumar NECO Ta Fadi Adadin Makarantu da Suka Yi Satar Amsa

  • Hukumar shirya jarabawa ta ƙasa (NECO) ta bayyana adadin makarantun da aka samu da laifin yin satar jarabawa a 2024
  • Shugaban hukumar NECO ya bayyana cewa makarantu 40 ne a cikin jihohi 17 aka samu da laifin satar jarabawar sakandaren
  • Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ya bayyana cewa an samu ɗalibai 8,437 da laifin satar jarabawa daban-daban a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Minna - Magatakardar hukumar shirya jarabawar ta ƙasa (NECO), Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi, ya yi magana kan satar jarabawar da aka yi lokacin zana jarabawar SSCE ta shekarar 2024.

Farfesa Dantani Wushishi ya bayyana cewa makarantu 40 ne aka samu da laifin yin satar jarabawa a lokacin jarabawar kammala sakandare ta sheƙarar 2024 (SSCE).

Kara karanta wannan

NECO 2024: Ɗalibai sun samu gagarumar nasara, fiye da 60% sun ci Turanci da Lissafi

NECO ta fadi makarantun da suka yi satar amsa
Makarantu 40 NECO ta samu da laifin satar jarabawa Hoto: @neconigeria, Nony and Sons
Asali: UGC

Makarantu sun yi satar jarrabawar NECO

Jaridar Tribune ta ce shugaban na hukumar NECO ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a birnin Minna na jihar Neja a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na hukumar NECO ya bayyana cewa an samu satar jarabawar ne a cikin jihohi 17, kuma makarantun za su fuskanci matakan ladabtarwa.

Ya kuma bayyana cewa an samu raguwar satar jarabawa da kaso 30.1% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

Ɗalibai sun rage satar jarabawar NECO

Ya yi bayanin cewa a shekarar 2024, ɗalibai 8,437 aka samu da laifin satar jarabawa daban-daban, wanda hakan bai kai yawan ɗalibai 12,030 da aka samu a shekarar 2023 ba.

"Ɗalibai 8,437 aka samu da laifin satar jarabawa daban-daban a shekarar 2024 saɓanin ɗalibai 12,030 a shekarar 2023 wanda hakan ya nuna an samu raguwar kaso 30.1%."

Kara karanta wannan

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024, an yi bayanin ka'idojin dubawa

"A lokacin gudanar da jarabawar SSCE ta 2024, an samu makarantu 17 da laifin satar jarabawa na bai ɗaya a jihohi 17."
"Za a gayyato su domin tattaunawa sannan bayan nan za a ɗauki matakan da suka dace."

- Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi

Matakan duba jarabawar NECO

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaliban da suka zana jarabawar NECO ta 2024 za su iya duba sakamakonsu ta hanyar shiga shafin yanar gizo hukumar.

Ɗaliban da suka zana jarabawar NECO kuma suke son duba sakamakonsu, za su yi amfani da lambar rajista, lambar sirri da shekarar jarabawar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng