Ana Wahalar Rayuwa, Gwamna a Arewa Ya Ware N22bn domin Aikin Samar da Ruwa
- Gwamnatin Katsina ta ware kuɗi N22bn domin aikin samar da wadataccen ruwan sha a faɗin kananan hukumomi 34
- Shugaban hukumar ruwa ta Katsina, Tlllle ya bayyana hakan, ya ce aikin zai kawo ƙarshen ƙarancin ruwa da rashin tsaftarsa
- Wannan aiki za a yi shi karkashin kulawar wani shiri na haɗin guiwa tsakanin gwamnatin Katsina da bankin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnatin Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa ta ware N22bn domin aikin samar da ruwa a faɗin kananan hukumomi 34.
Gwamnatin ta ce ta ware waɗannan maƙudan kuɗi ne domin tabbatar da samar da ruwan sha mai tsafta ga al'ummar jihar Katsina.
Manajan Datakta na hukumar ruwa ta Katsina, Tukur Hassan ne ya bayyana hakan ranar Laraba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙarancin ruwa zai zama tarihi a Katsina
A cewarsa, suna sa ran wannan aikin zai kawo ƙarshen kalubalen ƙarancin ruwa da rashin tsaftar ruwan sha a faɗin jihar.
Tukur Hassan ya ce:
"Muna da manyan ƙalubale guda biyu waɗanda muke ƙoƙarin shawo kansu a yanzu. A farko akwai bukatar mu fahimci wannan aiki da aka kinkimo, kusan mun gama da wannan batu."
"Haka nan kuma duk wani aikin (ruwa) da aka yi a wani wuri, ana bukatar al'ummar wannan yankin su kula da shi domin ya ɗore."
Aikin zai gudana a ƙarƙashin SURWASH
Shugaban sashen ayyukan samar da ruwan sha na shirin SURWASH, Aminu Dayabu ya ce hukumar za ta karbi N17bn daga cikin kuɗin da gwamnati ta ware don fara aikin.
Ya bayyana amfanin wannan aiki a rayuwar mutane, yana mai nuni da tsare-tsare da ka’idojin da gwamnati ta shinfiɗa domin aikin ya gudana a lungu da saƙon Katsina.
SURWASH wani shiri ne na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin Katsina da bankin duniya don samar da ruwa ga al'ummar jihar, rahoton Katsina Post.
Wani ɗan Katsina kuma manomi, Muhammad Bello ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan muhimmin aiki ne da Katsinawa ke matuƙar buƙata.
A cewarsa, bayan wahalar ruwan sha da ake yi, manoman da ke noman rani kamarsa, suna bukatar isasshen ruwan da za su yi aikinsu cikin daɗin rai.
Muhammad ya ce:
"Sanin kanka ne muna ƙarancin ruwa a Katsina, da zaran damina ta wuce ruwa ke ja baya, mu da muke noman rani duk shekara abun ƙara ja baya yake.
'Kuma na san mafi yawancin mutanen Katsina za su yi farin ciki da wannan aiki, fatan mu dai kar ya zama labarin takarda kawai, mu ji amma ba zamu gani a ƙasa ba."
Gwamnatin Katsina ta tura tallafi ga Borno
Kuna da labarin Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya hada tawaga mai karfi zuwa jihar Borno domin jajanta musu a kan ambaliyar ruwa.
An ruwaito cewa tawagar ta hada da mai martaba Sarki Daura, kakakin majalisar jihar da wasu jami'an gwamnatin Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng