Kumallon Mata: Wata Matar Aure a Kano Ta Zuba Fiya Fiya a Abincin Ɗan Kishiyarta

Kumallon Mata: Wata Matar Aure a Kano Ta Zuba Fiya Fiya a Abincin Ɗan Kishiyarta

  • An gurfanar da wata matar aure a gaban kotun majistire kan zargin kashe ɗan kishiyarta ta hanyar amfani da fiya-fiya
  • Mai gabatar da ƙara Barista Abdussalam Dan Maidaki Sale ya ce ana zargin matar da zuba maganin ƙwari a abincin yaron
  • Mai shari'a Hajara Safiya Hamza ta ɗage shari'ar zuwa ranar 30 ga watan Oktoba saboda kotun ba ta da hurumin sauraron ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - An cafke wata matar aure bisa zargin zuba guba a abincin ɗan kishiyarta ɗan kimanin shekara ɗaya tal a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta gurfana a gaban kotun majistire mai zama a Nomansland a ƙaramar hukumar Fagge bisa tuhume-tuhumen da suka shafi kisa.

Kara karanta wannan

Wani matashi ya 'kashe' budurwar da zai aura Naja'atu Ahmad a jihar Kano

Kotun Majistire.
Kano: An gurfanar da wata mata a kotu kan zargin kashe dan kishiyarta da guba Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Kano: Yadda matar ta kashe yaron kishiya

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, matar da ake zargin ta zuba maganin kashe ƙwarin da aka fi sani da fiya-fiya a abincin ɗan ƙaramin yaron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya zama sanadin mutuwar jaririn da bai wuce shekara ɗaya da haihuwa ba, wanda ba a kai ma ga yaye shi ba.

Lauyan masu shigar da kara, Barista Abdussalam Dan Maidaki Sale shi ne ya gabatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa matar wanda suka ta'allaka kan kisan kai.

Ya shaidawa kotun cewa laifin da ake zargin matar ta aikata ya saɓa wa tanadin sashe na 221 da ke ƙunshe a kundin dokokin Fenal Kod.

Wane mataki kotu ta ɗauka?

Sai dai kotun majistire ta bayyana cewa ba ta da hurumin sauraron wannan shari'a bisa tanadin dokokn kotunan majistire.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da wani shugaban al'umma

Bisa wannan dalili ne alƙalin kotun mai shari'a Hajara Safiya Hamza ta ɗage zaman zuwa ranar 30 ga watan Oktoba, 2024.

Amma gabanin haka ta bayar da umarnin a iza ƙeyar matar da ake zargin zuwa gidan gyaran hali kafin zuwan wannan rana.

Kano: An kama matashin da ya kashe budurwa

A wani rahoton kuma ƴan sanda sun kama wani matashi, Abubakar Kurna da ake zargi da kashe budurwar da zai aura a Kano.

Kotun majistire mai zama a Nomansland ta ba da umarnin a garƙame shi a gidan gyaran hali daga nan zuwa watan Nuwamba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262