Bayan Tallafin Biliyoyi, Gwamnatin Borno Ta Fitar da Gudunmawar Ambaliya da Ta Samu

Bayan Tallafin Biliyoyi, Gwamnatin Borno Ta Fitar da Gudunmawar Ambaliya da Ta Samu

Bayan samun tallafin biliyoyin kudi daga daidaikun mutane, yan siyasa da kungiyoyi, gwamnatin Borno ta ce an samu abinci mai tarin yawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Gudunmawar ta biyo bayan iftila’in ambaliya da ta shafi sama da mutane Miliyan biyu a Maiduguri, babban birnin jihar.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Borno
Gwamnatin Borno ta samu tallafin abinci saboda ambaliya Hoto: Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Jaridar aminiya ta wallafa cewa daga cikin wadanda su ka tallafa wa gwamnatin Babagana Umara Zulum da kayan abinci akwai hukumar raya yankin Arewa maso Gabas.

1. Tallafin kayan abinci da aka kai Borno

The Cable ta wallafa cewa hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta bayar da tallafin buhun shinkafa 20,000 da jarkar man girki 10,000 da kwalin taliya guda 20,000.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 kafin zabe, gwamnan Edo ya raba kyautar Naira biliyan 1 ga mata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin Sumal Food Group da ke Ibadan ya tallafa da Sinkin burodi 50, 000 da biskit 5,000, sai Hon Aminu Jaji ya bayar da tallafin shinkafa buhu 600.

A sanarwar da hadimin gwamnan Borno kan kafafen yada labarai, Abdurrahman Bundi ya fitar, ya ce jihar Nasarawa ta bayar da tallafin tirelar shinkafa guda biyu, na taliya guda biyu da na sukari shi ma tirela biyu.

Alhaji Abdulkadir Ali na Matrix Energy ya ba da tallafin kayan abinci na N120m.

2. An ba da tallafin taki bayan ambaliya a Borno

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, Janar Muhammad Buba Marwa mai ritaya ya bayar da gudunmawar tirela 10 na takin zamani da kudinsa ya kai N120m.

Ana sa ran wannan zai taimaka wa manoman a jihar bayan ambaliya ta wanke gonakin manoman Maiduguri.

Kara karanta wannan

Daga ƙarshe, an bayyana yawan tirelolin shinkafar da shugaba Tinubu ya turo Kano

3. Gwamnatin Borno ta samu tallafin tufafi

Kungiyar injiniyoyi ta kasa reshen jihar Borno ta bayar da tallafin turmi 10,000 na atamfa, shi ma Injiniya Usman Monguno ya ba da turmi 10,000 na atamfa.

A na ta bangaren, hukumar kula da aikin injiniya ta kasa da ta bayar da gwanjon tufafi masu nauyin kilo 400.

Ambaliya: Remi Tinubu ta tallafa wa Borno

A baya mun wallafa cewa Oluremi Tinubu, mai dakin shugaban kasa Bola Tinubu, ta ziyarci Maiduguri domin jajanta wa al'umar Borno kan iftila'in ambaliya da ta same su.

Oluremi Tinubu da ta samu wakilcin mai dakin mataimakin shugaban kasa ta mika tallafin Naira Miliyan 500 domin a tallafa wa wadanda su ka rasa muhallansu yayin ambaliyar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.