Kano: Gwamna Abba Ya Dauki Mataki kan Shugabannin Riko a Kananan Hukumomi 44
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya rusa shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 44 da ke jihar nan take
- A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan ya fitar, rushewar ta shafi ciyamomi, mataimakansu sakatarori da kansiloli
- Rushe shugabannin riƙon dai na zuwa ne yayin da ake tunkarar zaɓen ƙananan hukumomin jihar wanda za a gudanar a Oktoba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kawo ƙarshen wa'adin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar.
Gwamna Abba ya rusa shugabannin riƙon na ƙananan hukumomi 44 na jihar nan take.
Gwamna Abba ya rusa shugabannin riƙo
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rushewar dai na zuwa ne mako guda bayan da majalisar dokokin jihar ta amince da yi musu ƙarin wa’adi na tsawon wata biyu.
Wa'adin mulkin shugabannin riƙon dai tun da ya farko ya kamata ya ƙare ne a ranar, 8 ga watan Satumban 2024.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne aka shirya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.
Wane umarni Gwamna Abba ya ba su?
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci shugabannin riƙon da su miƙa ragamar shugabanci ga daraktocin kula da ma’aikata na ƙananan hukumomin.
A cewar sanarwar, rushewar ta shafi dukkanin shugabannin ƙananan hukumomi, mataimakansu, sakatarori da kansiloli.
Gwamna Abba ya nuna godiya ga shugabannin riƙon bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban yankunansu, ya kuma yi nuni da cewa akwai yuwuwar ya sake yin aiki da su a nan gaba.
Hukumar zaɓen Kano ta rage kuɗin fom
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe ta jihar Kano (KANSIEC), ta ɗauki matakin rage kuɗin siyan fom domin tsayawa takara a zaɓen kananan hukumomin jihar.
Shugaban hukumar, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki dangane da zaɓen ƙananan hukumomin wanda za a gudanar a watan Oktoba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng