Kano Ta Samu Cikas da Aka Gano 'Yan Kasuwa Sun Fitar da Gurbataccen Abinci Kasar Waje

Kano Ta Samu Cikas da Aka Gano 'Yan Kasuwa Sun Fitar da Gurbataccen Abinci Kasar Waje

  • Wasu 'yan kasuwar abinci ta Dawanau da ke Kano sun jawo wa tsarin fitar da kaya kasar waje cikas bayan an same su da matsala
  • Kwantena akalla 50 ce ta kayan abinci da aka fitar kasashen ketare aka gano su na da matsaloli daban daban
  • Wannan ta sa 'yan kasuwar duniya su ka dawo wa Dawanau da kwantenar kayan abincin, yayin da hukumomi su ka fara bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Masu sayen kayayyaki a kasashen waje sun yi watsi da kayan abinci da aka kai masu daga Najeriya saboda algus.

Kara karanta wannan

Ana batun kara haraji, gwamnoni 20 sun runtumo bashin Naira biliyan 446

A ranar Laraba ne aka dawo wa da kasuwar Dawanau kwantenar kayan abinci guda 50 da aka kai kasashen waje saboda zargin gurbatattu ne.

Kano map
Yan kasuwar Kano sun kai gurbataccen abinci kasuwar duniya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Punch ta wallafa cewa shugaban kasuwar, Alhaji Muntaka Isa ya ziyarci kasuwar domin ganin kayan da aka samu dawo da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yi takaicin dawo da kwantena Kano

Shugaban kasuwar Dawanau, Muntaka Isa ya bayyana irin koma baya da dawo da kwantenar kayan abinci 50 zai haifar da fitar da kayan kasar nan kasashen waje.

Ya kara da cewa wannan al'amari zai kawo nakasu ga kokarin da ake yi na ganin kasar nan, musamman manoman Kano sun zama yan kasuwar duniya.

Kano: NDLEA ta dauki mataki kan algus

Mahukuntan kasuwar xxxxxxxDawanau da ke Kano sun yi tir da yadda wasu 'yan kasuwa su ka hada gurbataccen kayan abinci zuwa kasar waje.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bude wuta, an damke masu taimakon 'yan bindigan Arewa da makamai

Shugaban kasuwar ya ce sun fitar da matakan da za su hana irin wannan, kuma za su dauki wasu matakan domin ladabtar da wadanda aka kama da laifi.

Kano: Farashin kayan abinci ya fara sauka

A baya mun ruwaito cewa farashin kayan abinci ya fara sauka a wasu kasuwannin da ke jihar Kano, musamman kasuwar hatsi ta Dawanau, inda farashin masara da gero ya yi kasa.

Shugaban kungiyar yan kasuwar, Mustapha Maikalwa ne ya tabbatar da haka, tare da bayyana fatan farashin zai ci gaba da sauka saboda jiran sabon kayan abinci daga gonakin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.