Bankin FCMB da Gidauniyar Tulsi Chanrai Sun Warkar da Makafi 150,000 a Kebbi

Bankin FCMB da Gidauniyar Tulsi Chanrai Sun Warkar da Makafi 150,000 a Kebbi

Bankin FCMB da hadin guiwar Gidauniyar Tulsi Chanrai sun warkar da masu matsalar ido 150,000 a jihar Kebbi.

Tun 2009, shirin ke ba da magani kyauta ga masu matsalar ido wurin yi musu aiki kyauta.

Daga cikin wadanda suka samu aikin tiyata kyauta na idanu a Kebbi da FCMB ta kaddamar
A gefen hagu, likitan Tulsi Chanrai, Dr. Mahesh Rao, sai Galadiman Gwandu, Alhaji Ibrahim Bashar da kwamishinan lafiya a Kebbi, Kwamred Yunusa Ismail da sauran mutane yayin shirin. Hoto: FCMB.
Asali: Facebook

Shirin ya warkar da mutane da dama da ya haɗa duka kananan hukumomi 21 da ke jihar.

A wani shirin da aka yi a karo na 15, matar gwamnan jihar, Hajiya Nafisa Idris ta godewa FCMB da Gidauniyar wurin kawo waraka ga masu matsalar ido.

"Mu na godiya ga FCMB da Tulsi Chanrai game da ba da waraka ga masu matsalar idanu wurin dawo musu da rayuwa mai amfani."

- Hajiya Nafisa Idris

FCMB ta kaddamar da aikin tiyatar idanu kyauta a Kebbi
Mutanen da suka ci gajiyar aikin warkar da matsalar idanu kyauta da bankin FCMB da Gidauniyar Tulsi Chanrai ta dauki nauyi a jihar Kebbi karo na 15. Hoto: FCMB.
Asali: Facebook

Shugaban tawagar FCMB, Diran Olojo ya ce bankin ya himmatu wurin tabbatar da ba da agaji ta hanyar shirye-shirye da suka shafi gani.

Ya ce shirin ya shafi yan Najeriya 400,000 a jihohin Kebbi da Cross River da Ogun da Imo da Katsina da Adamawa da sauransu.

Wani da yaci gajiyar, Muhammad Maganda ya fadi yadda ya koma makaho da kuma yadda idanunsa suka dawo bayan yi masa aiki.

Sai kuma Fatima Abdullahi ta nuna godiya da kuma jin dadi kan wannan aiki da aka yi mata tare da samun dawowar idanunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Legit.ng Branded Content avatar

Legit.ng Branded Content (marketing page) This account is used for publishing branded/sponsored content. For any enquiries please email: ads@corp.legit.ng or call: +234 810 304 48 99