An Shiga Fargaba, Ambaliyar Ruwa Ta sake Tafka Ɓarna a Jihar Borno

An Shiga Fargaba, Ambaliyar Ruwa Ta sake Tafka Ɓarna a Jihar Borno

  • Ambaliyar ruwa ta sake barna a jihar Borno inda ta wargaza wata babbar hanya da ake hada hadar yau da kullum a kanta
  • Shugaban karamar hukumar Damboa, Ali Muhammad Kauji ya ce wargajewar hanyar zai iya shafar jigilar abinci a sassan Borno
  • Legit ta tattauna da wani mazaunin Damboa domin jin yadda wargajewar hanyar zai shafi al'ummar yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - An sake samun mummunar barna saboda ambaliyar ruwa a tsakanin kananan hukumomin Konduga da Damboa a jihar Borno.

An ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta faru ne bayan wani ruwan sama mai karfi da aka tafka a ranar Talata da ta wuce.

Kara karanta wannan

Borno: Manya na ci gaba da zuwa jaje Maiduguri, an ƙara bada tallafin N50m

Ambaliyar ruwa
Ambaliya ta wargaza hanya a Borno. Hoto: Ahmad Usman Ajigin
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ruwan ya wargaza babbar hanyar zuwa karamar hukumar Damboa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ambaliya ta wargaza hanya a Borno

Ambaliyar ruwa ta sake barna a kan hanyar Damboa wacce ta ke kusa da ƙauyen Dalwa a karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa hanyar ta rabu gida biyu inda abubuwan hawa suka rika canza hanya domin samun damar wucewa.

An nemi taimako kan ambaliyar ruwa

Shugaban karamar hukumar Damboa, Ali Muhammad Kauji ya yi kira na musamman kan kawo dauki domin gyara hanyar da gaggawa.

Ali Muhammad Kauji ya bukaci gwamnati ta gyara hanyar da wuri domin kaucewa ƙaruwar barnar da jefa mutane cikin tsanani.

Amfanin hanyar Damboa ga mutanen Borno

Shugaban karamar hukumar Damboa ya bayyana cewa hanyar ita ce ta haɗa kudancin Borno da Maiduguri.

Haka zalika ya bayyana cewa yawancin kayan abinci a Maiduguri ana samo su ne daga karamar hukumar Damboa wanda hakan ke nuna muhimmacin gyara hanyar.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: 'Yan siyasa sun zabura, majalisar wakilai ta tallafa da N100m

Legit ta tattauna da Usman Ahmad Ajigin

Wani mazaunin Damboa, Usman Ahmad ya ce mutanen Damboa suna noma karas, tumatur, attaruhu da lemo da sauransu kuma ta hanyar suke tafiya zuwa Maidugiri.

Usman Ahmad ya kara da cewa mutanen Damboa, Chibok da Askira suna amfani da hanyar wajen kai kaya Maiduguri da kuma saro kaya.

A karkashin haka ya ce idan mutum zai yi zagaye domin zuwa Maiduguri ta wata hanya sai ya shiga ta wasu yankunan Adamawa wanda zai iya kwana a hanya.

UN ta ba mutanen Borno tallafin $6m

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayar da tallafin $6m ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa kodinetan UN a Najeriya, Mohammed Fall ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng