Malaman Firamare Sun Tsunduma Yajin Aiki, Suna shirin Zanga Zanga a Abuja

Malaman Firamare Sun Tsunduma Yajin Aiki, Suna shirin Zanga Zanga a Abuja

  • Malaman firamare a birnin tarayya Abuja sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bayan gargaɗi da suka yi ga gwamnati
  • Shugaban kungiyar malamai a birnin tarayya Abuja, Kwamared Ameh Baba ya ce sun tafi yajin aikin ne saboda hakkokin su da aka rike
  • Haka zalika Kwamared Ameh Baba ya ce nan gaba kadan malaman sakandare za su mara musu baya wajen tafiya yajin aiki a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Malaman makarantar firamare a birnin tarayya Abuja sun tsunduma yajin aiki kan rike musu hakkokinsu.

Yara yan makaranta sun nufi makarantu a yau Laraba amma sai aka maido su gida a kan cewa an fara yajin aiki.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bude wuta, an damke masu taimakon 'yan bindigan Arewa da makamai

Abuja
Malaman firamare sun tafi yajin aiki a Abuja. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa kungiyar malamai ta NUT ta tabbatar da suna shirin daukan wasu matakai bayan yajin aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin tafiyar malaman firamare yajin aiki

Malaman sun ce sun tafi yajin aikin ne domin saka hukumomi su biya su wasu hakkokin da aka rike musu na albashi.

Malaman sun ce an gaza biyansu alawus na kaso 40% da kuma karin albashi na kaso 25% da 35% da aka yiwa malamai.

Malamai sun yi gargadi kafin yajin aiki

Pulse Nigeria ta wallafa cewa malaman makarantar sun tafi yajin aikin ne a Abuja bayan sun ba gwamnati wa'adin kwanaki 14.

Kwamared Ameh Baba ya ce ilimin firamare shi ne tushen karatu saboda haka ya kamata a ba shi muhimmanci sosai.

Malaman firamare za su yi zanga zanga

Shugaban NUT ya ce idan gwamnati ba ta saurare su ba za su fito zanga zanga kuma malaman sakandare za su mara musu baya.

Kara karanta wannan

Mutuwar yan Maulidi 40 ta kaɗa Buhari, ya tura saƙo na musamman

Haka zalika Kwamared Ameh Baba ya ce idan aka yi kwanaki bakwai ba tare da an saurare su ba, za su rufe wasu ma'aikatun gwamnati.

ASUU ta tafi yajin aiki a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU) a jami'ar jihar Gombe ta tsunduma yajin aiki sakamakon rashin biyan bukatu.

Shugaban ASUU na jami'ar jihar Gombe, Dakta Salihu Sulaiman Jauro ya bayyana abubuwan da gwamnati ta gaza yi musu tsawon shekaru.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng