Kwanaki 3 kafin Zabe, Gwamnan Edo Ya Raba Kyautar Naira Biliyan 1 ga Mata

Kwanaki 3 kafin Zabe, Gwamnan Edo Ya Raba Kyautar Naira Biliyan 1 ga Mata

  • Gwamnan Edo, Godwin Obaseki ya tallafa wa mata yan kasuwa a jihar domin nuna jin dadin goyon baya da su ka ba shi
  • Gwamna Obaseki ya kara da cewa ana sa ran tallafin zai amfanar da su duba da hauhawar farashin kaya saboda tsadar fetur
  • A nuna goyon bayansu, matan a karkashin jagorancin shugabarsu, Blacky Ogiamien sun ce za su zabi PDP a ranar Asabar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo - Ana saura kwanaki uku gabanin zaben gwamna a Edo, gwamnan jihar, Godwin Obaseki ya raba tallafi ga mata 'yan kasuwa.

Gwamnan ya bayyana aniyarsa ta raba kyautar kudin a taron shekara-shekara da mata magoya bayan Obaseki su ka hada a Benin.

Kara karanta wannan

Jama'a sun razana bayan jami'ai da bindigu sun yi awon gaba da kantoma a Kano

Jihar Edo
Gwamnan Edo ya ba mata N1bn Hoto: Governor Godwin Obaseki
Asali: Facebook

AIT ta wallafa cewa wakilan mata yan kasuwa daga kananan hukumomi 18 na jihar ne su ka zauna da gwamna Godwin Obaseki a birnin Benin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin raba tallafin N1bn ga matan Edo

PM News ta wallafa cewa gwamna Godwin Obaseki ya raba tallafin ne domin gode wa mata da nuna jin dadi kan goyon bayan da su ka bashi tun 2016.

Haka kuma ya na fatan tallafin zai taimaka ma su wajen habaka kasuwanci ganin yadda aka samu tsadar man fetur a fadin kasar nan.

Matan Edo sun gode wa gwamna Obaseki

Mata yan kasuwa sun yaba da kokarin gwamna Godwin Obaseki wajen ba su tallafin da suke fatan zai saukaka masu bayan hauhawar farashin kayayyaki.

Shugabar kungiyar yan kasuwa mata ta jihar Edo, Blacky Ogiamien ta dauki alkawarin cewa za su tabbata sun zabi dan takarar PDP, Asue Ighadalo a zaben Asabar.

Kara karanta wannan

Uwargidan gwamna ta ji tausayin talakawa, ta raba tallafin kudi ga mata 1575

Edo: Atiku Abubakar ya gargadi zaben APC

A baya mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasar nan a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gargadi mazauna jihar Edo kan zabar APC.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa bin APC mai mulkin kasa a zabe mai zuwa zai jefa jama'a a yunwa da karuwar matsin rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.