Tsohon Shugaba a APC Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Yadda Abacha Ya Yi Masa Fintinkau

Tsohon Shugaba a APC Ya Caccaki Tinubu, Ya Fadi Yadda Abacha Ya Yi Masa Fintinkau

  • Tsohon jigo a jam'iyyar APC, Salihu Lukman ya sake caccakar Bola Ahmed Tinubu kan yadda yake gudanar da mulkinsa
  • Salihu Lukman ya bayyana cewa Tinubu ko kaɗan ba ya bari ana ganinsa ballantana har a ba shi shawara ya ɗauka
  • Tsohon mataimakin shugaban APC na ƙasa ya ce hatta marigayi Sani Abacha ya fi bari a riƙa ganinsa fiye da Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Salihu Lukman, ya bayyana Bola Tinubu a matsayin wanda bai bari ana ganinsa.

Salihu Lukman ya kwatanta Tinubu da marigayi tsohon shugaban ƙasa, Sani Abacha, inda ya ce an fi samun damar ganin marigayin fiye da Tinubu.

Kara karanta wannan

Awanni bayan dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu ya kawo ziyara Arewa, bayanai sun fito

Salihu Lukman ya caccaki Tinubu
Salihu Lukman ya sake caccakar Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Salihu Lukman
Asali: Facebook

Lukman ya kawo shawarar yakar Tinubu

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa tsohon jigon na APC ya bayyana hakan ne a cikin wata wasiƙa da ya fitar a ranar Talata a birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Salihu Lukman ya kuma yi kira ga tsofaffin shugabannin ƙasa, Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida da kuma Janar Aliyu Gusau da su ɓullo da dabarun da za su kawar da APC daga mulki a 2027.

Ya ce a halin yanzu ƴan Najeriya na fuskantar wani mawuyacin hali saboda dimokuraɗiyyar ƙasar tana cikin halin ha'ula'i, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.

Me jigon APC yace kan Tinubu?

"Kasancewar gwamnatin dimokuraɗiyya ce, an yi tsammanin cewa za a iya ganin Shugaba Tinubu domin ba shi shawarwari."
"Sai dai kash, yana nuna cewa shi ne shugaban Najeriya wanda ya kulle ƙofofinsa ga masu son ganinsa. Hatta marigayi Sani Abacha an fi samun damar ganinsa fiye da Tinubu."

Kara karanta wannan

NMA ta hango wata matsala bayan ambaliya a Maiduguri, ta ba da mafita

"Dukkanin gwamnatocin soji da aka yi a baya sun nuna cewa ƙofofinsu a buɗe suke ga ƴan Najeriya domin karɓar shawarwari fiye da gwamnatin Shugaba Asiwaju Tinubu."

- Salihu Lukman

Tsohon jigon APC ya faɗi makomar Tinubu

A wani labarin kuma kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban APC na shiyyar Arewa maso Yamma, Salihu Lukman ya ce lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su farka daga barci.

Lukman ya ce kamar yadda ƴan Najeriya suka kawar da mulkin sojoji shekaru 25 da suka wuce, za su kawo ƙarshen mulkin Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng