Mutuwar Yan Maulidi 40 Ta Kaɗa Buhari, Ya Tura Saƙo na Musamman

Mutuwar Yan Maulidi 40 Ta Kaɗa Buhari, Ya Tura Saƙo na Musamman

  • Mutane a Najeriya na cigaba da nuna alhini sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya jawo mutuwar yan Maulidi a Kaduna
  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya shiga cikin sahun mutanen da suka nuna damuwa kan rasa rayuka da aka yi a hadarin
  • Muhammadu Buhari ya yi addu'ar samun rahama ga wadanda suka rasu tare da yin fatan samun sauki ga waɗanda suka ji rauni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna damuwa kan mutuwar masu Maulidi a jihar Kaduna.

An ruwaito cewa mutane 40 ne suka rasu yayin da suke tafiya taron Maulidi a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota.

Kara karanta wannan

Hadarin maulidi: Gwamnan Kaduna ya dimauta, ya daukarwa dangi lkawari

Buhari
Buhari ya yi ta'aziyyar yan Maulidi 40 da suka rasu a Kaduna. Hoto: Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Legit ta samo ta'aziyyar da shugaba Buhari ya yi ne a wani sako da tsohon shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Maulidi 40 sun mutu a Kaduna

A ranar Lahadi ta da gabata ne aka samu wani mummunan hadarin mota a jihar Kaduna wanda ya rutsa da mabiya darikar Tijjaniyya.

Rahotanni sun nuna cewa mutanen za su tafi taron Maulidi ne kuma akalla 40 sun rigamu gidan gaskiya, wasu da dama sun jikkata.

Buhari ya yi jaje ga yan Maulidi

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga gwamnatin jihar Kaduna da daukacin al'ummar jihar kan haɗarin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya kadu matuka kan rashin da aka yi wanda har rayuka 40 suka salwanta.

Maulidi: Buhari ya yi addu'a da ta'aziyya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana taya dukkan yan uwan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya a sanadiyyar hadarin takaici.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: Shugaba Tinubu zai nema wa jama'a taimako, ya kafa asusun tallafi

Sannan kuma ya yi addu'a ta musamman domin samun sauki ga waɗanda suka ji raunuka suke kwance a asibiti.

An yi hadarin mota a Ogun

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da al'ummar Musulmi ke jerin gwanon bikin Maulidi a Najeriya an samu haɗarin mota a titin Ijebu-Ode zuwa Benin.

An ruwaito cewa mutane 18 ne suka kone kurmus bayan wuta ta tashi a motar da ta yi hadarin, wasu da dama kuma sun jikkata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng