Hatsarin Jirgin Ruwa: Gwamnan Zamfara Ya Ba da Tallafin Makudan Kudi

Hatsarin Jirgin Ruwa: Gwamnan Zamfara Ya Ba da Tallafin Makudan Kudi

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ba da tallafin kuɗi ga iyalan mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a ƙaramar hukumar Gummi
  • Gwamna Dauda ya ba da gudunmawar N20m ga iyalan mutanen da hatsarin jirgin ruwan na ranar Asabar, 14 ga watan Satumban 2024 ya shafa
  • Sarkin Gummi ya bayyana cewa ba mutane 40 ba ne hatsarin jirgin ruwan ya ritsa da su kamar yadda aka yi ta yaɗawa tun da farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sanar da bayar da gudunmawar Naira miliyan 20 ga iyalan mutanen da hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a jihar. 

A ranar Asabar, an ba da rahoton mutuwar mutane 41 bayan wani jirgin ruwa da ke jigilar fasinjoji sama da 50 ya kife a ƙaramar hukumar Gummi ta jihar.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar dinkin duniya ta ba da tallafin dalolin kudi ga mutanen Maiduguri

Gwamnan Zamfara ya ba da gudunmawa
Gwamna Dauda ya ba da N20m saboda hatsarin jirgin ruwa a Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Gwamnan Zamfara ya ba da gudunmawa

Jaridar The Cable ta ce mataimakin gwamnan Zamfara, Mani Mummuni, wanda ya yi magana a madadin gwamnan a ranar Talata ya sanar da ba da gudunmawar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mani Mummuni ya je ƙaramar hukumar ne domin kai ziyara ga Sarkin Gummi, Lawal Hassan da iyalan mutanen da abin ya shafa, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar da haka.

Mataimakin gwamnan ya ce tallafin zai rage wahalhalun da iyalan mutanen da hatsarin ya shafa ke fuskanta, ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta dukufa wajen daƙile aukuwar irin hakan a nan gaba.

"Ba mutane 40 ba ne", Sarkin Gummi

A nasa ɓangaren, Sarkin Gummi ya yaba da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka na ba da tallafin.

Ya ƙara da cewa fasinjoji 20 ne hatsarin ya ritsa da su, saɓanin mutane 40 da aka riƙa cewa hatsarin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgin ruwa: Hukumar NEMA ta fadi adadin mutanen da aka ceto a Zamfara

Sarkin ya ce an kuɓutar da mutane bakwai yayin da kuma aka gano gawarwaki 13

Gwamnan Zamfara ya yi alhinin kifewar jirgi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaɗu kan mutuwar mutane sama da 40 sakamakon hatsarin jirgin ruwa.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a rafin Bakin Kasuwa na ƙauyen Uban Dawaki da ke ƙaramar hukumar Gummi a matsayin babban bala’i.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng