Shugaba Tinubu Ya Umarci Gwamnan CBN Ya Yi Murabus? An Samu Bayanai
- Fadar shugaban ƙasa ta yi magana kan rahoton cewa Bola Tinubu ya umarci gwamnan bankin CBN, Yemi Cardoso, ya yi murabus
- A cewar wata gajeruwar sanarwa daga fadar shugaban ƙasa, Shugaba Tinubu bai umarci Yemi Cardoso ya yi murabus daga kujerarsa ba
- Rahoton karyar ya yi iƙirarin cewa shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne saboda ci gaba da faɗuwar darajar Naira a kan Dala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta yi martani kan rahoton da ke cewa Bola Tinubu ya umarci gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya yi murabus.
Fadar shugaban ƙasan ta ƙaryata rahoton, wanda ya yi iƙirarin cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci Yemi Cardoso, ya yi murabus nan take.
Bola Tinubu ya musanta korar gwamnan CBN
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya musanta hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayo Onanuga ya bayyana cewa rahoton ƙarya ne sannan shugaban ƙasan bai bayar da wannan umarnin ba.
CBN: Me rahoton yake cewa?
A cewar rahoton da aka yaɗa, Tinubu ya umarci Cardoso da ya yi murabus daga muƙaminsa ne saboda ya kasa magance taɓarɓarewar tattalin arziƙin Najeriya, musamman faɗuwar darajar Naira.
Majiya mai tushe ta bayyana cewa, Cardoso wanda aka naɗa tare da goyon bayan Dattawan Yarbawa ya kasa cika alƙawarin da ya ɗauka na dawo da darajar Naira da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan.
Cardoso ya yi alƙawarin mayar da Naira tsakanin N700 zuwa N900 kan $1 zuwa ranar 29 ga watan Mayu, 2024.
Sai dai, a ƙarƙashin jagorancin Cardoso, Naira ta faɗi raga-raga inda ta faɗi daga N950/$1 a lokacin da aka naɗa shi zuwa N1645.626/$1 a ranar 12 ga watan Satumba, 2024.
Bankin CBN ya kori daraktoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban bankin Najeriya (CBN) ya sallami wasu manyan daraktoci daga mukamansu kwanaki.
Bankin na CBN ya dakatar da daraktocin ne waɗanda ke jagorantar NIRSAL, hukumar ba da tallafi da basussuka ga ƴan Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng