Ambaliya: Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Ba da Tallafin Dalolin Kudi ga Mutanen Maiduguri

Ambaliya: Majalisar Ɗinkin Duniya Ta Ba da Tallafin Dalolin Kudi ga Mutanen Maiduguri

  • Majalisar Dinkim Duniya (UN) ta bayar da tallafin $6m ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maidugurin jihar Borno
  • Kodinetan UN a Najeriya, Mohammed Fall ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2024
  • Ya ce tawagar wakilan UN, kungiyoyi masu zaman kansu NGO, da Red Cross sun ziyarci Maiduguri domin raba kayan agaji ga mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno - Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta bayar da gudunmuwar Dala miliyan 6 domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kodinetan sashin ayyukan jin ƙai na UN a Najeriya, Mohammed Fall ya fitar yau Talata, 17 ga watan Satumba, 2024.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Dattijon attajiri, Dantata ya tallafa wa Borno da sama da Naira biliyan 1

Ambaliyar Maiduguri.
Majalisar Dinkin Duniya ta ba da tallafin $6m ga waɗanda ambaliya ta shafa a Borno Hoto
Asali: Getty Images

Ya ce tawagar hadin gwiwa da ta kunshi hukumomin UN da kungiyoyin NGO da kungiyar agaji ta Red Cross, sun ziyarci birnin Maiduguri a karshen mako, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dinkin duniya ta je Maiduguri

A cewar Muhammad Fall, tawagar ta gana da mutanen da ambaliyar ta rutsa da su, kuma galibinsu sun zama ƴan gudun hijira, rahoton Punch

Ya ce mafi akasarin waɗanda ambaliyar ta yi wa illa sun taɓa zaman gudun hijira sakamakon matsalar ƴan tada kayar baya da jihar Borno ke fama da su.

Ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon kwararar ruwa daga madatsar ruwa ta Alau da ke da nisan mil 10 daga kudancin Maiduguri.

Borno: UN da ƙungiyoyi sun fara raba tallafi

"Mu da abokan hulɗarmu mun fara rabon abinci, mun fara ƙoƙarin kai agaji ta sama zuwa wurare da ba a iya zuwa saboda ruwa ya lalata hanya.

Kara karanta wannan

'Ka da mu zargi kowa': Tinubu ya bayyana abin da ya jawo ambaliyar Maiduguri

"Har ila yau muna kokarin samar wa mutane da tsaftataccen ruwa da tsaftace muhalli domin daƙile yiwuwar ɓarkewar cututtuka."

- Mohammed Fall.

Ya kara da cewa ma’aikatan ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya na aiki kafada da kafada da masu hannu da shuni domin samun karin tallafin kudade.

Ɗantata ya kai ziyara Maiduguri

A wani rahoton kuma gwamnatin Borno ta kara samun tallafi domin a hada karfi da karfe wajen tallafa wa mutanen da ambaliya ta shafa a Maiduguri.

A wannan jikon, Attajirin Dattijo, Alhaji Aminu Dantata ne ya bayar da tallafin Naira Biliyan 1.5 domin a tallafa wa jama'ar garin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262