Gwamna Ya Kori Kwamishinansa bayan Shekara 3, an Gano Dalilinsa

Gwamna Ya Kori Kwamishinansa bayan Shekara 3, an Gano Dalilinsa

  • Gwamnan jihar Anambra Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya kori kwamishinansa na yaɗa labarai daga kujerarsa
  • Majiyoyi daga gidan gwamnatin jihar sun bayyana cewa Gwamna Soludo ya kori Mista Paul Nwosu ne saboda rashin aiki da kyau
  • A cewar majiyoyin tuni an zaɓi wanda zai maye gurbin tsohon kwamishinan wanda majalisar dokokin jihar za ta tantance shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya kori kwamishinansa na yaɗa labarai, Mista Paul Nwosu.

Majiyoyi sun bayyana cewa Gwamna Soludo ya kori kwamishinan ne saboda rashin yin kataɓus a muƙaminsa.

Soludo ya kori kwamishina a Anambra
Gwamna Soludo ya kori kwamishina Hoto: Professor Charles Chukwuma Soludo
Asali: Twitter

Meyasa Gwamna Soludo ya kori kwamishinan?

Jaridar Vanguard ta ce wata majiya daga fadar gwamnatin jihar ta ce Gwamna Soludo ya gaji da rashin iya aikin Paul Nwosu.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Kalamam gwamnan PDP sun tayar da kura ana dab da fara zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce Gwamna Soludo ya lura da yadda ƙimar gwamnatinsa ke ƙara zubewa a ƙasa yayin da aka tunkarar zaɓen gwamnan jihar a shekara mai zuwa.

"A yanzu da nake wannan maganar, Mista Paul Nwosu ya kwashe kayansa daga ma’aikatar kuma muna jiran a sanar da korarsa a hukumance."

- Wata majiya

An daɗe ana ƙorafi kan kwamishinan

Jama’a da dama a jihar Anambra, ciki har da jami’an gwamnati, sun ce korar Nwosu ba ta zo da mamaki ba, inda suka ce tuni ya kamata a yi hakan.

A cewar wasu ƴan jarida a jihar Anambra, kusan shekaru uku da Gwamna Soludo ya kwashe yana mulki, kwamishinan bai taɓa yi wa ƴan jarida bayanin ayyukan gwamnati ba, ko kuma amsa tambayoyi ba.

A wajensu, Nwosu shi ne kwamishinan yaɗa labarai na jihar Anambra wanda bai taɓuka abin kirki ba tun lokacin da aka ƙirƙiro ta.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

An tattaro cewa Gwamna Soludo ya zaɓi wanda zai maye gurbin Nwosu wanda nan ba da jimawa ba majalisar dokokin jihar za ta tantance shi.

Gwamna Soludo ya musanta korar hadiminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo ya musanta korar ɗaya daga cikin hadimansa kan bidiyon gasar rawar 'gwo gwo ngwo’.

Gwamma Suludo ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa a wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Christian Aburime ya fitar ranar Litinin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng