Hatsarin Jirgin Ruwa: Hukumar NEMA Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Ceto a Zamfara

Hatsarin Jirgin Ruwa: Hukumar NEMA Ta Fadi Adadin Mutanen da Aka Ceto a Zamfara

  • Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta ce an ceto wasu daga cikin wadanda hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da su a Zamfara
  • Hukumar NEMA ta ce an samu nasarar ceto mutum biyar da ransu sannan an gano gawarwaki tara na mutanen da suka rasu
  • Ta bayyana cewa ana ci gaba da ƙoƙarin gano sauran mutanen da ke cikin jirgin waɗanda ba a ji ɗuriyarsu ba tun bayan da ya kife

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta yi ƙarin bayani kan hatsarin jirgin ruwan da ya auku a jihar Zamfara.

Hukumar NEMA ta ce an ceto mutane biyar tare da gano gawarwaki tara a hatsarin wanda ya auku a ranar Lahadi a rafin Mashayar Yandaga da ke ƙaramar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Seaman Abbas: Muhimman abubuwa 7 a labarin sojan ruwan da ya ja hankalin ƴan Najeriya

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Zamfara
An ceto mutane biyar a hatsarin jirgin ruwa a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

A cewar NEMA, jirgin ruwan da hatsarin ya ritsa da shi yana ɗauke da fasinjoji sama da 40 da matuƙansa a lokacin da ya kife da su sakamakon cika masa kaya da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me hukumar NEMA ta ce kan hatsarin?

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X a ranar Talata ta hannun shugaban sashin yaɗa labarai, Manzo Ezekiel, ya ce bayan aukuwar hatsarin, an tattaro masu aikin ceto waɗanda galibinsu masunta ne.

"Sun yi nasarar ceto mutane biyar da ransu. Abin baƙin ciki, an gano gawarwakin fasinjoji tara ya zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da aikin gano sauran."

- Manzo Ezekiel

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a gano sauran fasinjojin da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara ba.

Darakta janar ta hukumar NEMA, Zubaida Umar yayin da take jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Zamfara kan lamarin, ta shawarci masu tuƙa jiragen ruwa da su riƙa yin aiki da matakan kariya wajen gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Hatsarin jirgi: Gwamnan Zamfara ya kadu kan asarar rayukan mutum 40, ya ba da umarni

Gwamnan Zamfara ya yi alhinin hatsari

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaɗu kan mutuwar mutane sama da 40 sakamakon hatsarin jirgin ruwa.

Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a rafin Bakin Kasuwa na ƙauyen Uban Dawaki da ke ƙaramar hukumar Gummi a matsayin babban bala’i.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng