Seaman Abbas: Dattawan Arewa Sun Yi Tofin Allah Tsine kan Zargin Zaluntar Sojan Ruwa

Seaman Abbas: Dattawan Arewa Sun Yi Tofin Allah Tsine kan Zargin Zaluntar Sojan Ruwa

  • Kungiyar Northern Elders Forum ta bayyana takaicin labarin cin zarafin wani jami'in rundunar sojan ruwa, Seaman Abbas Haruna
  • Jami'in hulda da jama'a a NEF, AbdulAzeez Suleiman ya ce yadda aka samu labarin Husaina Iliyasu kan cin zarafin mijinta ya jawo damuwa
  • Sanarwa da AbdulAzeez Suleiman ya fitar, ta ce lamarin ya jawo tambayoyi kan gwadaben tafiyar da jami'an rundunar tsaron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Kungiyar Northern Elders Forum ta bayyana damuwa kan halin da jami'in rundunar sojin ruwa na kasa, Seaman Abbas Haruna ke ciki.

Kara karanta wannan

Labarin Husaina: Hedikwata ta yi magana kan zargin Janar da zalunci, an dauki mataki

Mai dakin jami'in sojan, Husaina Iliyasu ta bayyana wa jama'ar kasar nan cewa an tsare mijinta na tsawon shekara shida ba tare da sanar da laifinsa ba.

Husaina
NEF ta yi tir da cin zarafin sojan ruwa bayan matarsa ta koka Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

A martanin da ta yi, jaridar Leadership ta wallafa cewa kungiyar NEF ta ce akwai damuwa da alamomin tambaya kan yadda ake bautar da jami'an da ke kokarin kare martabar kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sojan ruwa bai yi mugun laifi ba," NEF

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa jami'in rundunar sojan ruwa, Abbas Haruna bai aikata wani mugun laifi da ya dace a ba shi horo mai tsanani ba.

Kungiyar NEF da ta fadi haka ta bayyana yadda Seaman Haruna ya tattaro musulman da ke bataliyarsa tare da gabatar da sallar Juma'a a matsayin manuniya kan jajircewarsa ga aiki.

NEF ta yi zargin cin zarafin sojan ruwa

Kara karanta wannan

"Ba fashe wa dam ta yi ba:" Gwamnati ta fadi ainihin dalilin ambaliya a Maiduguri

Kungiyar NEF ta zargi kwamandan Seaman Haruna, Lafkanal Kanal Muhammad S. Adamu da cin zarafin jami'in da ke karkashinsa, wanda hakan bai dace ba.

Kungiyar ta bayyana damuwa kan dakile Seaman Haruna duk da cewa aikin da ya ke yi na hada kan jami'an sojojin kasar nan ne.

Za a binciki MS Adamu kan Seaman Haruna

A baya mun ruwaito cewa hedikwatar tsaron kasar nan ta tabbatar da aniyar gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa jami'in sojan ruwa, Lafkanal Kanal Muhammad S. Adamu bisa cin zarafi.

Matar wani sojan ruwa da ke bataliyar MS Adamu, Husaina Iliyasu ce ta zargi babban jami'in sojan da cin zarafin mijinta, har ta kai ga ya samu cutar tabin hankali bayan tsare shi na shekara shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.