Ambaliyar Ruwa: Atiku ya Ziyarci Maiduguri, Ya Ba da Gagarumar Gudunmawa

Ambaliyar Ruwa: Atiku ya Ziyarci Maiduguri, Ya Ba da Gagarumar Gudunmawa

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyarar jaje a jihar Borno sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a jihar
  • Atiku a yayin ziyarar ta sa ya ba da gudunmawar N100m domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa
  • Atiku ya kuma yi kira ga abokansa da su ba da irin ta su gudunmawar domin tallafawa dubunnan mutanen da ambaliyar ruwan ta ritsa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya kai ziyarar jaje a Maiduguri saboda ambaliyar ruwa.

Atiku Abubakar ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 domin tallafawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana tallafin da za ta kaiwa mutanen Maiduguri

Atiku ya ba da gudunmawar N100m a Borno
Atiku ya ba da gudunmawar N100m saboda ambaliyar ruwa a Borno Hoto: @atiku
Asali: Facebook

Jaridar The Punch ta rahoto cewa Atiku ya ba da gudunmawar kuɗin ne yayin ziyarar da ya kai a birnin na Maiduguri.

Atiku ya ba da gudunmawa a Borno

Sanarwar ba da gudunmawar na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar ranar Lahadi.

Ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, a ziyarar tasa, ya kuma kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum a gidan gwamnati, inda a nan ne ya sanar da bayar da tallafin.

Atiku ya kuma yi kira ga tarin abokansa da su ba da irin ta su gudunmawar a ƙoƙarin da ake yi na tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Bayan isowarsa filin jirgin Maiduguri, Atiku ya samu tarba daga Sanatoci masu wakiltar Borno ta Arewa da Borno ta Tsakiya, Mohammed Monguno da Kaka Lawan.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa: Gwamna Zulum ya fadi babbar damuwarsa

A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya yaba da irin wannan ƙaramcin na jigon jam'iyyar PDP, inda ya nuna godiyarsa a madadin mutanen jihar Borno.

Zulum ya faɗi damuwarsa kan ambaliya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana babbar damuwar da yake da ita kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar.

Gwamna Zulum ya ce ya damu matuƙa da yadda wasu shugabannin ƙungiyar Boko Haram da ke zaman gidan yari suka tsere daga gidan yarin da ke Maiduguri sakamakon ambaliyar ruwan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng