Mulkin Tinubu: Ledar Taliya Ta Gagari Talaka, an Fara Raba Leda Don Sayen Kadan Rabi da Kwata
- Bidiyo ya yadu a kafar sada zumunta na yadda ake sayar da taliya da makaroni ba yadda aka saba gani ba a duniya
- An ga kullin taliya N100, inda jama’a ke saye don samun abin da za su sanya a baki; a dai kar a mutu
- Janye tallafin mai da tashin darajar dala na daga cikin abubuwan da ke kara farashin kayayyaki a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Najeriya - Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa ‘yan kasa na kukan yunwa, abubuwa na ci gaba da dagulewa.
Wani bidiyo ya nuna yadda ake siyar da kullin taliya da makaroni da bai kai ledar da kamfani ke sayarwa ba.
A bidiyon da aka yada a TikTok, an ga wani na cinikin daurin taliya, inda aka ce ana sayarwa a kan kudi N100. Haka nan farashin yake ga kullin makaroni.
Kalli bidiyon:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farashin ledar taliya a Najeriya
A halin da ake ciki, ledar taliya ta kai sama da N1000 a Najeriya, lamarin da ke kara jefa masu karamin karfi cikin yanayi mai zafi a kasar.
Hakazalika, ledar makaroni ta kai N1000, inda kadan daga ma’aikata a Najeriya ke iya saye don kaiwa bakin salati.
Babu wani nau’in kayan abinci da ‘yan Najeriya basu ga ya sauya farashi ba, musamman tun bayan hawan Tinubu mulki da kuma janye tallafin mai.
Albashin ma’aikata a Najeriya
A halin da ake ciki, wasu daga ma’aikatan Najeriya na karbar N70,000 a matsayin albashi, yayin da wasu ke karbar N30,000 wasu kuma N18,000.
Kungiyoyin kwadago sun sha bayyana kukansu kan cewa, albashin ba zai isa sayen kayan abinci ba balle biyan kudin makaranta da sauran bukatu.
Leburori da ke nema a kasuwa sun sha kwana da yunwa a Najeriya saboda tsadar kayayyaki da tashin farashin man fetur.
An haramta kungiyoyin kasuwanci
A wani labarin, Sarkin Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi ya haramta kungiyoyi da ke cikin kasuwannin garin gaba daya.
Basaraken ya dauki matakin ne domin dakile yawan tashin farashin kaya da ya ke zargin kungiyoyin.
Shugaban wata kasuwa a Ile-Ife da ke jihar Osun, Akinwande Olajire shi ya tabbatar da haka, kamar yadda Punch ta tattaro.
Asali: Legit.ng