Rahoton NBS: Google, Facebook da Sauran Kamfanonin Waje Sun Biya Harajin N2.55tn Ga Najeriya
- Gwamnatin Najeriya ta tatsi haraji mai yawan gaske daga hannun kamfanonin kasashen waje da ‘yan Najeriya ke hulda dasu
- Kamfanonin da suka biya wannan harajin sun hada da Facebook, Twitter da NetFlix da dai sauransu
- Duk da karbar haraji, ‘yan Najeriya na ci gaba da shan tasirin talauci da kuma karancin ayyukan ci gaba daga gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - A watanni shida na farkon 2024, kamfanin kasashen waje kamar su Google, NetFlix da Facebook sun biya N2.55tr ga gwamnatin Najeriya a matsayin haraji.
Wannan na nufin sun biya karin 158.76% daga N985.27bn da suka biya a watanni shida na farkon 2023.
A cewar rahoton NBS, an karbi harajin ne ta hanyar CIT da kuma VAT da ake tatsa daga sayayyar ‘yan Naeriya.
Adadin kudaden da tattara daga VAT da CIT
Punch ta ruwaito cewa, kaso mai yawa da ya kai akalla N1.72tr ya fito ne daga harajin CIT sai kuma N831.47bn da ya fito daga harajanin VAT.
Idan baku manta ba, hukumar tattara haraji ta Najeriya (FIRS) na matsa lamba wajen karbar haraji daga hannun kamfanoni tun 2020 yayin da ‘yan Najeriya ke kara kusantar kafafen yanar gizo.
Wasu daga cikin kamfanonin, kamar NetFlix, Facebook da Twitter na gudanar da harkokinsu ne a kasashen waje ba tare da ofis a Najeriya ba.
Kaso nawa ake karba na haraji daga kamfanonin waje
Duk da haka, gwamnatin Najeriya ta kakaba haraji kan ‘yan kasar da ke hawa shafukan domin aiwatar da sayayya.
Gwamnatin Najeriya ta aiwatar karbar 6% na haraji daga kamfanonin kasashen waje da ke harkallarsu ta yanar gizo kuma 'yan Najeriya ke amfani dasu a karkashin sabuwar dokar kudi ta 2021.
Kamfanonin da ke kan gaba wajen biyan irin wannan karajin sun kasance su Amazon da Alibaba wadanda ke kan gaba a duniya wajen sayayyar kayayyaki ta yanar gizo.
Sauyin da aka samu daga 2023 zuwa yanzu a 2024
A kididdigar rubu’in shekara, kudaden harajin CIT ya karu daga N598.13bn a rubu’in farko zuwa N1.12tr a rubu’i na biyu, wanda hakan ya nuna karuwar 87.2%.
A daya bangaren kuma, harajin VAT ya dan ragu kadan a rubu’i na biyu na shekarar zuwa N395.74bn, inda ya ragu da N435.73bn a rubu’in farko.
Ministan kudi na Najeriya Wale Edun ya bayyana cewa, kudaden shigar gwamnati gaba daya ya kai N9.1bn a cikin rubu’in 2024, wanda ya ninka adadin da aka tara a 2023.
Shin Najeriya na amfana da harajin da ake karba?
Wannan kari da gwamnatin Najeriya ke samu wajen taysar haraji ya nuna yadda kasar ke habaka karfin samun kudaden shiga ta hanyar harajin amfani da kafafen yanar gizo.
Sai dai, babban abin tambayar, ta ina ake yiwa talakawan kasar ayyukan da za su taimaka masu, duba da a Najeriya yanzu babu tallafin man fetur, ilimi, magani, wutar lantarki har ma da sufuri.
‘Yan Najeriya dai sun sha bayyana rokonsu kan a dawo musu da tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye.
Asali: Legit.ng