Jami'an Tsaro Sun Saki Sowore, Ya Bayyana Yadda Ta Kaya a Tsakaninsu

Jami'an Tsaro Sun Saki Sowore, Ya Bayyana Yadda Ta Kaya a Tsakaninsu

  • Jami'an tsaro na hukumar shiga da fice ta Najeriya sun saki Omoyele Sowore jim kaɗan bayan sun cafke shi a filin jirgin sama Murtala Muhammad da ke Legas
  • Sowore ya bayyana cewa jami'an sun sake shi ne sannan sun mayar masa da fasfo ɗinsa bayan sun tsare shi na wani ɗan lokaci
  • Jami'an hukumar dai sun cafke Sowore bayan ya shigo Najeriya daga ƙasar Amurka a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Jami'an tsaro sun saki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC a zaɓen shekarar 2023, Omoyele Sowore.

Jami'an tsaron sun sake shi ne bayan sun yi caraf da shi lokacin da ya shigo Najeriya daga ƙasar Amurka a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zangar Oktoba: DSS ta cafke ɗan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore

Jami'an tsaro sun saki Sowore
Jami'an tsaro sun saki Omoyele Sowore Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

An cafke Sowore a Legas

A cewar Sowore dai jami'an tsaro na hukumar kula da shige da fice ne suka cafke shi tare da tsare shi bayan ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sowore wanda ya bayyana hakan a wani rubuta da ya wallafa a shafinsa na X da safiyar Lahadi ya kuma ce an sake shi bayan wasu ƴan mintoci kaɗan.

Sowore wanda ya shirya zanga-zangar #RevolutionNow ya ce jami'an hukumar shige da fice ta Najeriya sun kwace fasfo ɗinsa tare da shaida masa cewa sun samu umarnin tsare shi.

Jami'an tsaro sun saki Sowore

"Yanzun nan jami'an hukumar shige ta fice ta Najeriya suka sake ni bayan sun tsare ni na ɗan gajeran lokaci sannan sun dawo min da fasfo ɗina."

Omoyele Sowore

Har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton, hukumomi ba su tabbatar ko musanta kama Sowore ba.

Kara karanta wannan

Kasurgumin ɗan bindiga Bello Turji ya turo saƙo kan harajin N50m da ya sa a Zamfara

Gwamnati ta janye daga tuhumar Sowore

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta janye tuhumar da ta ke yiwa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AAC a zaɓen shekarar, Omoyole Sowore.

Gwamnatin ta janye tuhumar ce da ta ke yi na zargin cin amanar ƙasa a kansa a a ranar Laraba 14 ga watan Faburairun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng