Shirin Zanga Zangar Oktoba: DSS Ta Cafke Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Omoyele Sowore

Shirin Zanga Zangar Oktoba: DSS Ta Cafke Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Omoyele Sowore

  • Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kama tsohon dan takarar shugaban kasar Najeriya, Omoyele Sowore
  • An ce jami'an DSS sun cafke Sowore a ranar Lahadin lokacin da ya dura kasar a filin jirgin saman Murtala Muhammed an Legas
  • An ce kama Sowore ba zai rasa nasaba da kiran da ya yi na 'yan kasar nan su gudanar da zanga zangar adawa da wannan gwamnati ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) sun kama fitaccen mai fafutuka kuma mai shirya zanga-zangar Oktoba ta #RevolutionNow, Omoyele Sowore.

An kama Sowore ne ranar Lahadi a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, jim kadan bayan ya isowarsa Najeriya.

Kara karanta wannan

Yunwa: Wasu Gwamnonin jihohin Kudu sun fitar da tsarin wadata jama'a da abinci

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an DSS sun cafke Omoyele Sowore
Legas: An ce jami'an tsaron DSS sun cafke Omoyele Sowore kan shirya zanga zanga.
Asali: Twitter

DSS ta cafke Omoyele Sowore

Dan fafutuka kuma shugaban kungiyar Concerned Nigerians, Kwamared Deji Adeyanju ne ya tabbatar da kama Soworo ga jaridar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeyanju ya ce:

"Gwamnatin Najeriya ta marasa aikin yi da rashin bin doka da oda ta kama Sowore saboda kiran da ya yi na a gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin kama karya.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Sowore ya yi ikirarin cewa jami’an tsaron Najeriya na yunkurin kama shi a mahaifarsa ta Kiribo da ke karamar hukumar Ese-Odo, jihar Ondo.

NIS ta kwace fasfon Sowore

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na X, Sowore ya ce hukumar immigiration ta kwace fasfo dinsa.

“Na sauka filin jirgin MMIA a Legas daga Amurka; da isa ta wajen jami'an hukumar Immigration, an kwace fasfo dina kuma sun ce an ba su umarnin su tsare ni.”

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

“Wannan ba abin mamaki ba ne domin a hakan na daga cikin yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke yi wa ‘yan adawa da fargabar zanga zangar Oktoba da ke tafe.

Sowore ya roki 'yan Najeriya da su tabbata sun gudanar da zanga zangar da aka shirya yi a watan Oktoba ko da ace gwamnati ta tsawaita tsare shi da ta yi.

Jami'an tsaro sun damke Sowore

A wani labarin, mun ruwaito cewa dan fafutuka kuma tsohon dan takaran kujeran shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya shiga hannun jami'an tsaro a Abuja.

Kakakin jam'iyyar African Action Congress AAC, Femi Adeyeye, ya bayyana hakan inda ya ce an kama Sowore ne bayan fitowarsa daga wata kotu a ranar 24 ga watan Febrairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.