Bayan Cin Zarafin Wasu a Kano, DSS Ta Cafke Lakcara game da Zanga Zanga

Bayan Cin Zarafin Wasu a Kano, DSS Ta Cafke Lakcara game da Zanga Zanga

  • Ana zargin jami'an hukumar DSS a Najeriya sun kama wani lakcara a Jami'ar Baze da ke birnin Abuja, Dr. Abubakar Alkali
  • An wuce da Alkali ne zuwa jihar Sokoto fiye da makwanni uku kan zargin goyon bayan zanga-zanga da aka yi a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ana zargin hukumar DSS da cafke wani lakcara a Abuja kan tuhumar goyon bayan zanga-zanga.

Hukumar ta cafke Dr. Abubakar Alkali ne da ke Jami'ar Baze a Abuja saboda zargin hannu a zanga-zangar da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Girma ya fadi: Basarake ya shiga matsala, ana zarginsa da sace matashi da karbar N2.5m

Ana zargin DSS ta cafke wani lakcara a Jami'ar Abuja
Hukumar DSS ta kama wani lakcara a Jami'ar Abuja kan zargin goyon bayan zanga zanga. Hoto: AANUFAMO Photography.
Asali: Facebook

Lauya ya zargi DSS da cafke lakcara

Fitaccen lauya a Abuja, Deji Adeyanju shi ya tabbatar da haka a jiya Asabar 14 ga watan Satumbar 2024 a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeyanju ya ce an cafke Alkali ne makwanni uku da suka wuce inda aka wuce da shi jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.

Lauyan ya ce ana zargin Alkali da goyon bayan zanga-zanga wanda har yanzu yana kulle bai fito ba.

Zargin da DSS ke yi wa lakcara

"Jami'an DSS sun dauke Dr. Abubakar Alkali, lakcara a Jami'ar Baze da ke Abuja makwanni uku da suka wuce."
"An wuce da Dr. Alkali zuwa jihar Sokoto kan zargin goyon bayan zanga-zanga, ana cigaba da tsare shi har yanzu."

Deji Adeyanju

Leadership ta tura sakon karta-kwana ga hukumar DSS domin sanin halin halin da ake ciki amma babu martani.

Kara karanta wannan

PDP da Babban Sifetan yan sanda sun kai ruwa rana kan zaɓe, IGP ya fusata a bidiyo

Wani shugaban matasa ya fadawa Legit Hausa ra'ayinsa kan wannan mataki na hukumar DSS.

Kwamred Abdulkadir Abubakar ya ce akwai abubuwa da ya kamata DSS ta fi mayar da hankali a kansu.

"Ban ga dalilin kama mutum domin zanga-zanga ba, yaushe hakan ya zama laifi a ƙasa"?
"Ya kamata jami'an tsaro su sani muna mukin dimukraɗiyya ne ba wai na soja ba da babu mai yancin fadan abin da yake so."

- Kwamred Abubakar

DSS ta saki shugaban NLC, Ajaero

Kun ji cewa mintuna kafin wa'adin da kungiyar NLC ta ba gwamnatin Bola Tinubu ya cika, hukumar DSS ta saki Kwamred Joe Ajaero.

Kungiyar NLC da TUC sun yi barazanar dakatar da komai a kasar wanda suke ganin zai taba tattalin arziki idan ba a sake shi ba.

Hakan ya biyo bayan cafke Ajaero da DSS ta yi a birnin Abuja yana shirin zuwa Landan domin babban taron kungiyar kwadago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.