Kotu Ta Ba Aminu Ado Bayero Umarni kan Gyaran Fadar Nasarawa

Kotu Ta Ba Aminu Ado Bayero Umarni kan Gyaran Fadar Nasarawa

  • Shirin yin gyaran da Sarkin Kano na 15 yake yi a fadar Nasarawa ya samu cikas daga wajen babbar kotun jihar Kano
  • Babbar kotun ta jihar Kano ta hana Aminu Ado Bayero daga yin aikin gyara a fadar Nasarawa wacce yake zaune a cikinta tun bayan dawowarsa
  • Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Dije Abdu Aboki ta umarci ya dakatar da yin gyara a fadar har zuwa lokacin da za ta saurari ƙarar da aka shigar kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta hana Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, gyara fadar Nasarawa.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Dije Abdu Aboki, ta bayar da umarnin ne na wucin gadi wanda ya hana Sarkin yin gyara a fadar Nasarawa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan babban dan majalisar PDP ya riga mu gidan gaskiya

Kotu ta hana Aminu Ado yin gyara a Kano
Kotu ta hana Aminu Ado Bayero gyara fadar Nasarawa Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Aminu Ado Bayero dai ya kasance yana zaman fada a ƙaramar fadar tun bayan dawowarsa jihar bayan da gwamnatin jihar ta rusa masarautun jihar, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa suka shigar da ƙarar?

Gwamnatin jihar Kano ta hannun babban lauyanta da Masarautar Kano ne suka shigar da karar yayin da Aminu Ado Bayero ne kaɗai ake ƙara a cikin shari'ar.

Umarnin kotun ya buƙaci dukkanin ɓangarorin da ke cikin shari'ar da su bar komai yadda yake dangane da tsarin ginin fadar har zuwa lokacin da za ta saurari ƙarar tare da yanke hukunci.

Yaushe aka shigar da ƙarar?

Takardun kotun sun nuna cewa masu shigar da ƙarar sun shigar da ƙarar ne a ranar 9 ga watan Satumban 2024.

Kotun ta kuma umarci a kai wa Aminu Ado Bayero takardun kotu ta wata hanya ta daban sannan ta tsayar da ranar 2 ga watan Oktoban 2024 domin sauraron ƙarar.

Kara karanta wannan

Zaben Edo: Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game manyan ƴan takara 3

Aminu Ado ya yi gayyatar Maulidi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi gagarumar gayyata ta bikin Maulidi wanda za a gudanar a fadarsa da ke Nassarawa.

Basaraken ya gayyaci al'ummar Musulmi domin bikin murnar ranar zagayowar haihuwar fiyayyen halitta Manzon Allah (SAW).

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng