Dubu Ta Cika: An Kama Wani Dattijo Ɗan Shekara 74 Yana Sata a Masallaci
- Jama'a sun yi ram da wani ɗattijo ɗan shekara 74 wanda ke sace masu tabarmin masallacin unguwa a Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna
- Mutumin mai suna Jibril Musa ya amsa laifinsa, inda ya ce ya jima yana ƴan ɗauke-ɗauke a masallatai amma bai taɓa satar Alƙur'ani ba
- Jibril da ake zargi da laifin satar, ya bayyana hanyar da yake bi wajen satar, ya ce yana sayar da duk tabarma ɗaya a kan N1,500 zuwa N2,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Dubun wani dattijo ɗan shekara 74 a duniya, Jibril Musa da ke yawan sace-sace a Masallaci ya cika a unguwar Rigasa da ke ƙaramar hukumar Igabi a Kaduna.
Mazauna unguwar sun kama dattijon dumu-dumu yana satar tabarmun Masallacin da suke yin sallolin farilla.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, lamarin ya faru ne a layin Sarkin Bori Sule, inda mutane suka cafke dattijon kuma bai musa ba, ya masa laifinsa.
Kaduna: Yadda ɓarawon ya addabi Masallatai
Rahotanni sun bayyana cewa mazauna unguwar sun jima suna ƙorafin yawan sace-sacen tabarmi a Masallaci, hakan ya sa suka fara sa ido domin gano ɓarayon.
Bayan cafke shi, Jibiril Musa ya amsa laifinsa da cewa ya jima yana ɗauke-ɗauken tabarmi a Masallatai daban-daban a unguwar.
Ya kuma yi bayanin cewa wannan shi ne karo na biyu da ya saci tabarma a wannan Masallacin, kuma aka kama shi.
Dattijon da aka kama ya yi bayani
Da yake bayanin yadda yake fakar ido ya sace tabarmi, Jibril Musa ya ce:
"An kama ni da tabarmar da na sato a masallacin. Yadda nake yi shi ne, zan je sallar jam'i, idan mutane suka gama suka fita sai na kwashe sababbin tabarmu.
"Wasu lokutan na kan jira har sai kowa ya fita masallacin ya zama ba kowa sannan na kwashe tabarmun, wannan ne karo na biyu da na zo nan masallacin.
"Ina sayar da duk tabarma ɗaya da na sato kan N1,500 zuwa N2,000."
Dattijon ya bayyana cewa wani lokacin ya kan sace agogon Masallaci amma bai taɓa satar Alƙur'ani Mai Tsarki ba.
Kaduna: Ambaliya ta rusa gada
A wani rahoton kuma ambaliyar ruwa da ruguza gadar da ta haɗa garin Saminaka da wasu kauyukan manoma biyar a ƙaramar hukumar Lere ta Kaduna.
Kwamitin ambaliyar ruwa da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kafa ya kai ziyara yankin domin duba ɓarnar da ruwan ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng