Ana Wayyo Allah, 'Yan Kasuwa Sun kara Tunkarar Tinubu domin Cire Tallafin Fetur

Ana Wayyo Allah, 'Yan Kasuwa Sun kara Tunkarar Tinubu domin Cire Tallafin Fetur

  • Kungiyar yan kasuwar man fetur sun kara fuskantar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan wasu bukatu na musamman
  • Cikin abubuwan da yan kasuwar suka bukata akwai neman gwamnatin tarayya ta cire hannu a kan tallafin man fetur gaba daya
  • Sun bayyana cewa hakan zai ba yan kasuwar damar sayen man fetur daga ko ina kuma su saka farashin da ya dace a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar yan kasuwa sun kara tunkarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan maganar tallafin man fetur.

'Yan kasuwar sun bayyana dalilan da suka sanya su neman gwamnatin tarayya ta karasa cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwa sun gama karaya da matatar Dangote, sun fadi sharadin sayen fetur

Bola Tinubu
An bukaci Tinubu ya kammala cire tallafin man fetur. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa yan kasuwar sun yi magana kan ba matatun man fetur na cikin Najeriya muhimmanci domin farfaɗo da tattali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bukatar cire tallafin man fetur gaba daya

Yan kasuwar na man fetur sun tura sako ga shugaba kasa Bola Tinubu kan cire tallafin man fetur gaba daya.

Sun bayyana cewa hakan zai ba su damar shiga ko ina a kasashen duniya su sayo mai ba tare da saka bakin gwamnatin tarayya ba.

Amfanin cire tallafin man fetur a Najeriya

Kungiyar yan kasuwar ta ce cire tallafin man zai jawo wadatuwar man fetur a Najeriya a kowane lokaci.

Ta kuma kara da cewa hakan zai zaburar da yan kasuwa wajen yin rige-rigen tallata kayansu wanda hakan zai iya kawo saukin farashi.

Bukatar inganta matatun man Najeriya

Economic Confidential ta wallafa cewa kungiyar yan kasuwar ta nuna muhimmacin inganta matatun man fetur din cikin gida Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan Kudu da Arewa sun hada kai, sun tunkari Tinubu kan tsadar man fetur

Yan kasuwar sun bayyana cewa hakan zai jawo cigaba sosai a cikin gida da kuma rage dogaro da kasashen ketare.

An bukaci Tinubu ya rage kudin mai

A wani rahoton, kun ji cewa karin kudin man fetur a Najeriya na cikin abubuwan da suka cigaba da jan hankulan al'umma saboda wahala da aka shiga.

Kungiyoyi a Kudu da Arewacin Najeriya sun nuna takaici kan karin kudin man fetur da aka samu a Najeriya wanda hakan ya kara jefa mutane wahala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng