An Yi Rashi: Direban Mota Ya Hallaka Babban Jami'in 'Dan Sanda
- Wani direban mota ya yi aika-aika a jihar Ekiti bayan ya salwantar da ran wani babban jami'in dan sandan Najeriya
- Direban motar dai ya bi ta kan ɗan sandan ne lokacin da yake bakin aikinsa a wani shingen bincike a birnin Ado-Ekiti
- Rundunar ƴan sandan jihar ta bayyana cewa tana ƙoƙarin ganin ta cafke direban wanda ya arce bayan ya hallaka jami'in
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ekiti - Wani direban mota ya hallaka wani jami'in ɗan sanda mai matsayin ASP da ke aiki da rundunar ƴan sandan jihar Ekiti.
Jami'in ɗan sandan ya rasa ransa ne bayan direban ya bi ta kansa da motar da yake tuƙawa.
Ƴadda direba ya kashe ɗan sanda
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami’in mai suna Idris Lawal an murƙushe shi ne har lahira a wani shingen bincike da ke Ayemi Garage kusa da titin Iworoko a Ado-Ekiti, babban birnin jihar.
Lamarin ya faru ne a lokacin da jami'an ƴan sanda ke gudanar da aikin bincike da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Litinin, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.
Duk da cewa an garzaya da marigayin zuwa asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ekiti (EKSUTH) domin duba lafiyarsa, likitocin da ke bakin aiki sun tabbatar da rasuwarsa.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
A bayanin da ƴan sanda suka yi kan lamarin, an ajiye gawar marigayin a ɗakin ajiye gawarwaki domin bincike.
Ƴan sanda sun bayyana cewa motar da aka tafka wannan ta'asar da ita wata fara ce ƙirar Mercedes Benz.
Rundunar ƴan sandan ta kuma ƙara da cewa tana ƙoƙarin cafke mai laifin.
Ƴan bindiga sun hallaka jami'an tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro biyu a sakatariyar ƙaramar hukumar Isiala-Mbano da ke jihar Imo.
Ƴan bindigan sun mamaye yankin ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Talata inda suka yi ta harbe-harbe kan mai uwa da wabi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng