Ana cikin Halin Kunci, Jigon APC Ya Fadi Amfanin Manufofin Tinubu ga 'Yan Najeriya

Ana cikin Halin Kunci, Jigon APC Ya Fadi Amfanin Manufofin Tinubu ga 'Yan Najeriya

  • Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Delta ya fito ya ba ƴan Najeriya haƙuri kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan a mulkin Bola Ahmed Tinubu
  • Morrson Olori ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara kai zuciya nesa domin Shugaba Tinubu na bakin ƙoƙarinsa wajen ganin al'amura sun daidaita
  • Ya bayyana cewa manufofin da Shugaba Tinubu ya ɓullo da su a gwamnatinsa, ya kawo su ne domin ya tsamo ƴan Najeriya daga ƙangin talauci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Wani ɗan kasuwa kuma jigon jam'iyyar APC a jihar Delta, Morrison Olori, ya fito ya kare shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Morrison Olori ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu yayin da take ƙoƙarin magance halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar.

Kara karanta wannan

Joe Ajaero: Daga karshe gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin cafke shugaban NLC

Jigon APC ya kare Tinubu
Jigon APC ya kare Tinubu kan halin kuncin da ake ciki Hoto: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Me jigon APC ya ce kan Tinubu?

Jaridar The Punch ta rahoto cewa jigon na jam'iyyar APC ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a birnin Ughelli ranar Laraba.

"Tsare-tsaren da gwamnatin Tinubu ta ɓullo da su, ta kawo su ne domin ciro ƴan Najeriya daga ƙangin talauci."
"Waɗannan tsare-tsaren za su haifar da ɗa mai ido a nan gaba. Ziyarar da Tinubu ya kai China da sauran ƙasashe za ta jawo masu zuba hannun jari zuwa cikin ƙasar nan."
"Akwai masu zuba hannun jari ƴan ƙasashen waje da yanzu haka sun shigo cikin ƙasar nan, wanda hakan zai samar da ayyukan yi da ƙara bunƙasa abubuwan da ake samarwa."
"Dangane da halin da ake ciki a ƙasar nan, Shugaba Tinubu yana bakin ƙoƙarinsa domin ganin ya bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan tun bayan hawansa kan mulki."

Kara karanta wannan

APC ta kwancewa Tinubu zani a kasuwa kan tsadar rayuwa

- Morrison Olori

APC ta juyawa Tinubu baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɓullo da su sun ƙara taɓarɓarar da tattalin arziƙi.

A cikin wata sanarwa da kakakin jam'iyyar APC ya fitar, ya yi bayanin cewa sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya kawo sun kawo halin ƙunci a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng