Ana Jimamin Ambaliyar Maiduguri, Ruwa Ya Katse Garuruwa 5 a Jihar Kaduna

Ana Jimamin Ambaliyar Maiduguri, Ruwa Ya Katse Garuruwa 5 a Jihar Kaduna

  • Ambaliyar ruwa da ruguza gadar da ta haɗa garin Saminaka da wasu kauyukan manoma biyar a ƙaramar hukumar Lere ta Kaduna
  • Kwamitin ambaliyar ruwa da Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya kafa ya kai ziyara yankin domin duba ɓarnar da ruwan ya yi
  • Gwamna Uba Sani ya ce gwamnatinsa za ta gyara gadar kuma za ta samar da kayan tallafi ga mutanen da lamarin ya rutsa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Wata mummunar ambaliyar ruwa ta datse hanyar da ta haɗa garin Saminaka da wasu garuruwan manoma biyar a ƙaramar hukumar Lere ta jihar Kaduna.

Wata gada da ruwan ya ruguza a gefen garin Saminaka ta toshe titunan da mutanen ƙauyukan ke shiga hedikwatar ƙaramar hukumar Lere.

Kara karanta wannan

Wani Malamin Addini ya daɓawa matarsa wuƙa har lahira, gwamna ya ɗauki mataki

Taswirar Kaduna.
baliya ta riguza gada a karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gwamnan Kaduna ya fara ɗaukar matakai

Gwamna Uba Sani ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta dauki matakin gaggawa domin shawo kan lamarin, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya faɗi haka ne ta bakin shugaban ma’aikatansa, Malam Liman Sani Kila, wanda ya jagoranci kwamitin ambaliya zuwa karamar hukumar Lere.

Malam Sani Kila ya yi alkawarin cewa, baya ga sake gina gadar da ta ruguje, za a kuma samar da kayayayyakin agaji ga waɗanda ambaliyar ruwan ta rutsa da su.

Ambaliya: Uba Sani zai rabawa mutane tallafi

"Mun ga adadin ɓarnar da ambaliyar ta yi kuma mun fahimci ɗaukin gaggawar da ake buƙata, ruwa ya katse kauyuka biyar wanda hakan ya shafi harkokinsu na kasuwanci.
"Muna ƙara ba ku tabbacin Gwamna Uba Sani ya himmatu wajen magance matsalolin da mutane ke ciki, kuma kwamitinmu zai yi masa bayanin abin da ya faru a nan."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya bayyana adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Borno

- Malam Sani Kila.

Ciyaman na Lere ya yabawa gwamna

Shugaban karamar hukumar Lere, Mathew Bulus Gambo, ya nuna jin dadinsa kana ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa kafa kwamitin da zai magance matsalar.

Ya ce rugujewar gadar ta gurgunta harkokin kasuwancina yankunan da abin ya shafa, yana mai jaddada muhimmancin daukar matakin gaggawa, Channels tv ta rahoto.

Ruwa ya fara janyewa a Maiduguri

A wani rahoton kuma wasu daga cikin mazauna birnin Maiduguri sun fara ƙoƙarin komawa gidajen su bayan ruwan ambaliya ya janye da safiyar ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun fara tantance asarar da suka yi sakamakon ibtila'in wanda ya mamaye yankuna da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262