Borno: Mutanen Maiduguri Sun Wayi Gari da Labari Mai Daɗi bayan Ambaliyar da Ta Afku
- Wasu daga cikin mazauna birnin Maiduguri sun fara ƙoƙarin komawa gidajen su bayan ruwan ambaliya ya janye da safiyar ranar Laraba
- Rahotanni sun nuna cewa mazauna garin sun fara tantance asarar da suka yi sakamakon ibtila'in wanda ya mamaye yankuna da dama
- Gwamnatin Borno karkashin Babagana Umaru Zulum ta fara raba kayan agaji da kuɗaɗe domin taimakawa waɗanda lamarin ya rutsa da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Maiduguri, Borno - Rahotannin da muka samu sun nuna cewa mutane sun fara ƙoƙarin komawa gidajemsu yayin da ruwan ambaliya ya fara janyewa a Maiduguri.
An tattaro cewa galibin mutanen da ruwa ya raba da matsugunansu sun kwana ne a waje, wasu kuma sun samu mafaka a sansanin ƴan gudun hijira.
Ambaliya: Mutane sun fara tantance kayansu a Maiduguri
Vanguard ta ruwaito cewa mutanen da ibtila'in ya shafa sun bayyana cewa duk da ruwa ya janye, ba za su yi gaggawar komawa gida ba, za su tantance kayan da suka yi asara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai suna Ali Bana, mazaunin gundumar Gwange a jihar Borno ya ce:
"Muna gaggawa ne domin duba abin da ya rage a cikin gidajenmu sannan mu ɗauko sauran abubuwan da za su mana amfani ko a nan gaba."
Musa Abdullahi daga yankin Gumari ya ce ya samu zuwa gidansa amma har yanzu ruwa bai janye daga ciki ba.
A cewarsa, ga dukkan alamu shi da iyalansa za su ci gaba da kwana a waje har zuwa lokacin da ruwan zai janye gaba ɗaya.
Dubban mazauna Maiduguri sun shiga jarabawa
Rahoton da ofishin ayyukan jin ƙai na majalisar dinkim duniya (OCHA) ya fitar ya ce ambaliyar ruwan ta raba dubban mutane akalla 239,000 da matsugunansu.
“Ambaliyar ta tilasta wa wasu mutanen kaura zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Muna, wanda dana yana dauke da ‘yan gudun hijira sama da 50,000."
Hukumar dillancin labarai NAN ta ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta katse sadarwa, wutar lantarki, da ruwan sha a mafi yawan sassan garin Maiduguri.
Zulum ya fara agazawa mutane
A wani rahoton kuma Gwamna Babagana Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki game da ambaliyar ruwan da ta afku a Maiduguri da wasu yankuna a Borno.
Zulum ya fara rabawa mutanen da suka rasa matsugunansu kayan agaji da tsabar kudi, ya ba da kwangilar dafa masu abinci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng