An Rasa Rayukan Mutum 9 a Wani Hatsarin Mota kan Titin Zaria Zuwa Kano

An Rasa Rayukan Mutum 9 a Wani Hatsarin Mota kan Titin Zaria Zuwa Kano

  • Wani mummunan hatsarin mota da ya auku a jihar Kano ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum tara har lahira
  • Kakakin rundunar kiyaye haɗurra ta ƙasa reshen jihar Kano ya ce hatsarin ya auku ne a tsakanin wata babbar mota da adaidaita sahu
  • A cewar Abdullahi Labaran hatsarin da ya ritsa da mutum 12 ya auku ne a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba a ƙaramar hukumar Kura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Aƙalla mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a kan hanyar Kano zuwa Zaria.

Wasu mutane uku sun kuma samu raunuka daban-daban a hatsarin wanda ya auku a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da ƴan sanda sun mamaye fadar Sarki bayan fara raɗe raɗin ya rasu

Hatsarin mota ya auku a Kano
Mutum tara sun rasu sakamakon hatsarin mota a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Kakakin hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), reshen jihar Kano, Abdullahi Labaran ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashar TVC ta rahoto cewa aukuwar hatsarin ya jawo sauran motoci sun samu tsaiko wajen wucewa.

Yadda hatsarin motar ya auku

Kakakin ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a ranar Laraba 11 ga watan Satumba, 2024 a ƙaramar hukumar Kura ta jihar Kano.

Abdullahi Labaran ya bayyana cewa hatsarin ya ritsa da mutane 12 ne waɗanda ke cikin wata babbar mota da adaidaita sahu.

"Abin takaici mutane tara ne suka rasa rayukansu a hatsarin, yayin da mutum uku suka samu raunuka. Nan take aka kwashe waɗanda abin ya shafa zuwa babban asibitin Kura domin samun kulawar gaggawa."
"Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa hatsarin ya auku ne sakamakon gudun wuce gona da iri wanda ya sanya motar ta ƙwace."

Kara karanta wannan

Ambaliyar Maiduguri: NEMA ta bayyana adadin mutanen da suka rasu a jihar Borno

"Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Kano, Ahmed Mohammed, ya jajantawa iyalan waɗanda suka rasu da waɗanda suka samu raunuka."

- Abdullahi Labaran

Mutane sun rasu a hatsarin mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 16 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a babbar hanyar Ore zuwa Ondo a jihar Ondo.

Hatsarin wanda ya auku a ƙauyen Ajue da ke kan titin, ya haɗa da motoci biyu, wata motar bas ƙirar Toyota Hiace da wata babbar mota.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng