Gwamna Zulum Ya Bayyana Adadin Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a Borno
- ki ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su
- Farfesa Zulum ya bayyana cewa ambaliyar ruwan da ta auku a ranar Talata ta shafi mutane miliyan ɗaya
- Ya bayyana cewa ya kafa kwamitin lafiya domin daƙile yaɗuwar cututtuka a birnin Maiduguri da Jere
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce adadin mutane miliyan ɗaya ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Ambaliyar ruwan da ta auku a ranar Talata ta yi sanadiyyar raba mutane da matsugunansu a birnin Maiduguri da kewaye
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne ga manema labarai, yayin da yake raba kuɗade da dafaffen abinci ga ƴan gudun hijirar da suka samu mafaka a sansanin Bukassi da ke birnin Maiduguri, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Wane ƙoƙari gwamna Zulum ke yi?
Gwamnan ya ce an kafa kwamitin lafiya na bayar da agajin gaggawa domin daƙile yaɗuwar cututtuka a Maiduguri da birnin Jere, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Kun ga yadda ruwa ya mamaye yankin gaba ɗaya, magudanun ruwa sun cika, hakan na nufin za a iya kamuwa da cututtuka masu yaɗuwa amma Insha Allahu za mu shawo kan lamarin."
"Har ya zuwa yanzu dai ba mu iya tantance yawan ɓarnar da aka samu ba, amma kusan kaso ɗaya bisa huɗu na ɗaukacin birnin Maiduguri na cike da ruwa."
"Mutanen da abin ya shafa sun kai miliyan ɗaya, abin da muke yi a safiyar yau shi ne samar da agajin gaggawa, wanda ya haɗa da ba da abinci da sauran kayayyaki"
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Ndume ya nuna alhini kan ambaliyar ruwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno.
Sanata Ndume ya jajantawa jama’a da gwamnatin jihar Borno, sakamakon aukuwar ambaliyar ruwan da ta mamaye gidaje da dama a wasu sassan birnin Maiduguri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng