‘Ka Ba Mu Kunya:’ Shugaban Yarabawa Ya Tura Zazzafar Wasika ga Tinubu
- Al'umma a fadin Najeriya na cigaba da kokawa kan yadda lamura ke tafiya a Najeriya karkashin mulkin Bola Tinubu
- Wani shugaban Yarabawa, Iba Gani Adams ya tura wasika ga Bola Ahmed Tinubu kan halin da talaka ke ciki a Najeriya
- Iba Gani Adams ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba yan Najeriya kunya yadda ya mayar da kasar a kasa da shekaru biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban Yarabawa na Aare Ina Kakanfo, Iba Gani Adams ya tura wasika mai zafi ga Bola Tinubu.
Iba Gani Adams ya tura wasikar ne yana kokawa kan yadda rayuwa ta yi tsanani a Najeriya musamman ga talakawa.
Vanguard ta wallafa cewa Gani Adams ya ce yan Najeriya sun yi tsammanin Bola Tinubu zai kawo canji amma abubuwa sun dagule.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ba yan Najeriya kunya inji Gani
Gani Adams ya ce a lokacin da Bola Tinubu ya ci zaɓe a 2023 an yi tsammanin zai tabuka abin kirki a Najeriya.
A cewar Gani Adams, a kasa da shekaru biyu shugaba Bola Tinubu ya ba yan Najeriya kunya kan yadda ya gaza kawo sauyi kuma aka shiga tsadar rayuwa.
Gani: 'Ba mu gane gyaran Tinubu ba'
Tribune ta wallafa cewa Gani Adams ya ce a lokacin da Tinubu ya hau mulki man fetur yana da sauki amma yanzu lita ta kai N1,000.
Gani ya kara da cewa farashin Dala ya karu a kan Naira kuma a hakan wai ana gyara, ya tambayi cewa 'Wane irin gyara ne a haka?'
Magana kan kama masu zanga zanga
Gani Adams ya ce bayan tsananin rayuwa ta yi yawa yan Najeriya sun fito zanga zanga domin nuna bacin rai a watan Agusta.
Amma sai dai a cewarsa, abin takaici gwamnati ta kama su da sunan wai sun aikata laifin cin amanar kasa.
An bukaci rage kudin man fetur
A wani rahoton, kun ji cewa karin kudin man fetur a Najeriya na cikin abubuwan da suka cigaba da jan hankulan al'umma saboda wahala da aka shiga.
Kungiyoyi a Kudu da Arewacin Najeriya sun nuna takaici kan karin kudin man fetur da aka samu a Najeriya a makon da ya wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng