Ambaliya: Mutane Sama da 200,000 Sun Rasa Gidaje, Yara Sun Bace a Maiduguri

Ambaliya: Mutane Sama da 200,000 Sun Rasa Gidaje, Yara Sun Bace a Maiduguri

  • Bayanai sun fara fitowa kan irin asarar da aka tafka a Maiduguri sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta mamaye garin
  • Rahotanni da suka fito na nuni da cewa mutane sama da 200,000 ne suka rasa gidajen zamansu sakamakon ambaliyar ruwan
  • Haka zalika iyaye da dama sun koka kan rashin ganin ƴaƴansu wanda ana hasashen cewa yaran sun nitse ne a cikin ruwan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Mazauna Maiduguri sun fara lissafa irin asarar da suka yi bayan mummunar ambaliyar ruwa.

An samu bayanai kan adadin mutanen da suka rasa gidajensu a birnin Maiduguri a ambaliyar ranar Talata.

Ambaliyar ruwa
An rasa dubban gidaje yayin ambaliya a Borno. Hoto: Bulama Adamu
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa har yanzu ba a samu adadin yaran da suka bata a cikin garin Maiduguri ba.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa da aka wayi gari da su a Maiduguri bayan ambaliya

Mutane 200,000 sun rasa gidaje a Maiduguri

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa gidaje a Maiduguri.

Hakan ya faru ne sakamakon ambaliyar ruwan da ta kutsa cikin gidaje, kasuwanni da gonakin al'umma.

Yara sun bata sakamakon ambaliyar ruwa

Al'umma da dama sun gaza ganin yaransu da yan uwansu da ambaliyar ruwa ta afka musu a Maiduguri.

Wata mata mai suna Fatima Ali ta bayyana cewa ta samu kubuta da kyar amma har yanzu bata ga kannenta shida ba.

Haka zalika wata mata da ake kira Ya'ana ta ce tun karfe 3:30am aka tayar da ita domin neman mafita amma har yanzu ba ta san inda yaran ta suke ba.

The Sun ta wallafa cewa hukumomi sun tabbatar da batan yara sakamakon ambaliyar sai dai har yanzu ba a fitar da adadin yaran da suka bata ba a hukumance.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

Dabbobi sun mutu yayin ambaliyar Maiduguri

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar gidan dabbobi a Maiduguri ta fitar da sanarwa bayan ambaliya ta shiga gidan tare da tafiya da dabbobi masu yawan gaske.

Babban manajan gidan dabbobin ya bayyana cewa wasu dabbobi masu hadari da yawa sun shiga cikin al'umma saboda haka aka bukaci yin taka-tsan-tsan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng