Joe Ajaero: Daga Karshe Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Cafke Shugaban NLC

Joe Ajaero: Daga Karshe Gwamnatin Tinubu Ta Fadi Dalilin Cafke Shugaban NLC

  • Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta yi magana kan dalilin da ya sanya jami'an tsaro suka cafke Joe Ajaero
  • Gwamnatin ta bayyana cewa an cafƙe shugaban na ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ne saboda ya ƙi amsa gayyatar hukumomin tsaro
  • Ta kuma musanta zargin da aka yi mata na take haƙƙin ɗan Adam sakamakon tsare Ajaero da jami'an tsaro suka yi a farkon makon nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin take haƙƙin ɗan Adam da ƙungiyar ƴan kasuwa (TUC) ta Birtaniya ta yi mata kan tsare shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero.

Gwamnatin tarayyar ta haƙiƙance cewa babu wanda ya fi ƙarfin doka a Najeriya ciki har da shugaban na ƙungiyar NLC.

Kara karanta wannan

APC ta kwancewa Tinubu zani a kasuwa kan tsadar rayuwa

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan cafke Joe Ajaero
Gwamnatin tarayya ta fadi dalilin cafke shugaban NLC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X.

Meyasa aka cafke Joe Ajaero?

A cikin sanarwar, Onanuga ya ce jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun kama shugaban na NLC ne saboda yaƙi amsa gayyatar da jami’an tsaro suka yi masa.

"An zargi gwamnatin Najeriya bisa kuskure da ƙarya kan take haƙƙin ɗan Adam saboda an hana shugaban NLC, Joe Ajaero tafiya ƙasar waje bayan da ya ƙi amsa gayyatar wata hukumar tsaro da ke gudanar da bincike."
"A bayyane yake, a ƙarƙashin kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), babu wani mutum da ya fi ƙarfin gayyata daga hukumomin tsaro da binciken da ke bisa doka."

Kara karanta wannan

Kin shiga zanga zanga ya yi riba, gwamna ya ba matasa kyautar N310m

"A matsayinsa na ɗan Najeriya mai kishin kasa, ya kamata Mista Ajaero ya mutunta duk wata gayyata daga hukumomin tsaro da kuma magance duk wata matsala da za ta taso a yayin gudanar da bincike."

- Bayo Onanuga

Hukumar DSS ta saki Joe Ajaero

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta sako shugaban ƙungiyar kwadago na ƙasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero da tsakar dare.

Hukumar tsaron ta saki shugaban ƙungiyar ƙwadagon ne ƴan mintuna kaɗan kafin wa'adin da NLC ta ba gwamnatin Bola Tinubu ya cika.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng