Kin Shiga Zanga Zanga Ya Yi Riba, Gwamna Ya Ba Matasa Kyautar N310m

Kin Shiga Zanga Zanga Ya Yi Riba, Gwamna Ya Ba Matasa Kyautar N310m

  • Gwamnan Akwa Ibom ya cika alƙawarin da ya ɗauka na kyautatawa matasan jihar idan suka ƙi shiga zanga-zanga
  • Mai girma Gwamna Umo Eno ya ba da kyautar N310m domin rabawa ga matasa a ƙananan hukumomi 31 na jihar Akwa Ibom
  • Ya bayyana cewa yana sane da halin ƙuncin da ake ciki kuma yana bakin ƙoƙarinsa domin magance hakan a jiharsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya sanar da ba da kyautar tsabar kuɗi N310m ga shugabannin matasan jihar.

Gwamna Umo Eno ya ba da kyautar kuɗin ne waɗanda za a raba a ƙananan hukumomi 31 na jihar saboda ƙin shiga zanga-zangar #EndBadGovernance da aka gudanar a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

A ƙarshe Shugaba Tinubu ya faɗi ayyukan da yake yi da kudin tallafin man fetur

Gwamna Eno ya ba da kyautar N310m
Gwamna Akwa Ibom ya ba matasa kyautar kudi Hoto: Umo Eno
Asali: Facebook

Gwamna Uno ya ba da kyautar N310m

Jaridar The Punch ta rahoto cewa gwamnan ya ba da sanarwar ne lokacin da yake jawabi a wajen wani taron gangamin nuna godiya da aka gudanar a filin wasan ƙwallon ƙafa na Uyo a ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa kowace daga cikin ƙananan hukumomi 31 na jihar za ta samu N10m, rahoton jaridar New Telegraph ya tabbatar.

Meyasa gwamna ya ba da kyautar kuɗin?

Gwamna Umo Eno ya ba da kyautar kuɗin ne domin cika alƙawarin da ya ɗauka ga matasan cewa zai kyautata musu idan ba su shiga zanga-zangar ba.

Gwamnan ya ƙara da cewa za a raba kuɗaɗen ne a tsakanin jam'iyyu.

"Shugabannin matasa a kowace ƙaramar hukuma za ta karɓi kuɗin sannan su raba a tsakanin jam'iyyu."
"Ba za mu ƙyale ku yadda muka same ku ba. Mun ji daɗi sosai cewa kun ji kiran da muka yi muku na ka da ku shiga zanga-zangar, ba wai domin ba mu yarda da cewa ana cikin halin ƙunci ba."

Kara karanta wannan

Duk da suna adawa, gwamnan Sokoto ya ba PDP shawara kan zaben ciyamomin jihar

"Mun fahimci cewa akwai ƙalubale irinsu yunwa, rashin aikin yi da tsadar kayayyakin abinci. Za mu yi bakin ƙoƙarin mu wajen magance hakan a iya ƙarfin da muke da shi a matakin jiha."

- Gwamna Umo Eno

Zanga-zanga ta ɓarke a Bauchi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar zanga-zanga ta ɓarke a garin Zaranda Gari da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Zanga-zangar ta ɓarke ne a ranar Talata, 10 ga watan Satumban 2024 biyo bayan kashe wasu mutane biyu da wani mafarauci ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng