Ana Jimamin Ambaliyar Ruwa a Borno, Gini Ya Rufto kan Mutane a Birnin Kudu
- Ruftowar wani gini da ta auku a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa ta jawo asarar rayukan mutum uku
- Jami'an ƴan sanda waɗanɗa suka kai ɗaukin gaggawa a wajen da lamarin ya auku sun yi nasarar ciro mutum bakwai
- Kakakin rundunar ƴan sandan jihar wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana cewa an miƙa gawarwakin ga iyalan domin birne su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Jigawa - An samu asarar rayuka bayan wani gini ya rufto a ƙaramar hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa.
Mutum uku ne suka rasa rayukansu biyo bayan ruftawar ginin da ta auku a rukunin gidajen Kofar Bai Quarters.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kakakin rundunar ƴan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Adam, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Talata.
Yadda gini ya rufto kan mutane a Jigawa
Ya bayyana cewa wani mutum mai suna Ahmad Isah ya kawo rahoto ga ofishin ƴan sanda na Birnin Kudu cewa wani ɗaki a gidansa ya rushe.
DSP Lawan ya bayyana cewa bayan samun rahoton, an tura tawagar jami'an ƴan sanda zuwa wurin da lamarin ya auku.
Ya nuna cewa ƴan sanda tare da taimakon wani bawan Allah sun samu nasarar ciro mutum bakwai daga ginin da ya rushe.
An rasa mutane da ginin ya fado
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa lokacin da aka kai mutanen zuwa asibiti, an tabbatar da mutuwar mutum uku.
Ya bayyana sunayen waɗanda suka rasu a matsayin Khalifa Ahmad mai shekara 13, Tijjani Ahmad mai shekara 12 da Rabiu Ahmad mai shekara 12.
A cewarsa an miƙa gawarwakin zuwa ga iyalan domin birne su kamar yadda addinin musulunci ya tanada yayin da ake duba lafiyar sauran mutum huɗun a asibiti.
Gini ya rufto a Legas
A wani labarin kuma, kun ji cewa mutum biyar sun rasu sakamakon ruftawar wani gini da ke lamba 13, kan titin Wilson Mba, a unguwar Maryland da ke Legas.
Ginin da ake yi ya ruguje ne da misalin ƙarfe 3:49 na safiya a unguwar Maryland da ke jihar Legas a yankin Kudancin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng