Ambaliyar Ruwa: Sanata Ndume Ya Nuna Alhininsa, Ya Ba Gwamnati Shawara

Ambaliyar Ruwa: Sanata Ndume Ya Nuna Alhininsa, Ya Ba Gwamnati Shawara

  • Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya nuna alhininsa kan iftila'in ambaliyar ruwan da ta auku a birnin Maiduguri na jihar Borno
  • Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya bayyana cewa ya kaɗu matuƙa bayan samun labarin irin ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yi
  • Ali Ndume ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo ɗauki ga mutanen da abin ya shafa domin aikin ya fi ƙarfin gwamnatin jiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Tsohon mai tsawatarwa na majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume, ya nuna alhininsa kan ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Borno.

Sanata Ndume ya jajantawa jama’a da gwamnatin jihar Borno, sakamakon aukuwar ambaliyar ruwan da ta mamaye gidaje da dama a wasu sassan birnin Maiduguri, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Borno: Muhimman wurare 5 da ambaliyar ruwa ta fi yin barna a Maiduguri

Ndume ya kadu kan ambaliyar ruwa a Borno
Sanata Ali Ndume ya bukaci a kai dauki ga mutanen Borno Hoto: Sen. Mohammed Ali Ndume
Asali: UGC

Jaridar The Punch ta ce ya yi wannan alhinin ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Abuja ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Ndume ya ce kan ambaliyar ruwa?

Sanata Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kai ɗauki tare da tallafawa gwamnatin jihar wajen bayar da agaji ga mutanen da abin ya shafa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Sanatan ya bayyana cewa ya damu matuƙa da labarin da ya ji dangane da irin ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yi.

Ali Ndume ya buƙaci hukumomi da su tashi tsaye domin kawo ɗauki ga mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a Maiduguri.

Sai dai ya koka kan cewa ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yi ta wuce gwamnatin jiha ta magance ta, saboda haka akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo ɗauki.

Kara karanta wannan

Bayan iftila'in Maiduguri: Gwamnati ta dauki sabon matakin magance ambaliyar ruwa

Ambaliya ta sa an rufe jami'ar UNIMAID

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukuntan jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno sun ɗauki matakin rufe ta har sai abin da hali ya yi.

An rufe jami'ar ne biyo bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta mamaye sassan birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Mahukunta jami'ar sun kuma jajantawa ma'aikata da ɗaliban ɗa ambaliyar ruwan ta shafa tare da addu'ar Allah ya kiyay aukuwar hakan nan gaba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng