Ambaliyar Ruwa: Mahukuntan Jami'ar UNIMAID Sun Dauki Matakin Gaggawa
- Ambaliyar ruwan da aka samu a birnin Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta jawo an rufe jami'ar UNIMAID
- Mahukuntan jami'ar sun sanar da hakan domin kare ɗalibai da ma'aikata sakamakon ambaliyar da ta auku
- Sun kuma miƙa saƙon jaje ga ɗalibai da ma'aikatan da ambaliyar ta ritsa da su tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Mahukuntan jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno sun ɗauki matakin rufe makarantar har sai abin da hali ya yi.
An rufe jami'ar ne biyo bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta mamaye sassan birnin Maiduguri, babban birnin jihar.
Jaridar Daily Trust ta ce hukumar gudanarwar jami’ar ta sanar da rufe jami’ar na wucin gadi ne a wata sanarwa da magatakardar ta, Ahmad A. Lawan ya fitar a ranar Talata.
An rufe jami'ar UNIMAID saboda ambaliya
A cikin sanarwar an jajantawa ma’aikata da daliban da iftila'in ambaliyar ruwan ya shafa.
"Ana sanar da ma'aikata da ɗalibai cewa sakamakon ambaliyar ruwan da ta shafi Maiduguri, hukumar jami'a ta dakatar da karatu tare da rufe ofisoshi na wucin gadi ba tare da ɓata lokaci ba har sai al'amura sun daidaita."
"An ɗauki matakan ne domin kare ma'aikata da ɗalibai tare da yin duba kan lamarin kafin ɗaukar matakan da suka dace."
"Ana miƙa saƙon jaje ga ɗaukacin ma’aikata da ɗaliban da bala’in ambaliyar ruwan ta shafa tare da addu’ar Allah ya kiyaye aukuwar hakan nan gaba.”
- Ahmad A. Lawan
Ambaliyar ruwan dai na da nasaba da ɓallewar madatsar ruwa ta Alau da ake zargin ta cika tun mako guda da ya wuce.
Ƴan gidan yari sun tsere a ambaliya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaurarrun da ba a kai ga sanin adadinsu ba sun samu damar tserewa daga kurkukun da aka ajiye su a jihar Borno.
Ƴan gidan yarin sun samu arcewa daga inda ake tsare da su ne sakamakon mummunar ambaliyar ruwan da aka samu a birnin Maiduguri.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng