An Rasa Rayuka Bayan Zanga Zanga Ta Barke a Jihar Bauchi

An Rasa Rayuka Bayan Zanga Zanga Ta Barke a Jihar Bauchi

  • Wasu fusattun matasa sun fito kan tituna a garin Zaranda Gari da ke ƙaramar hukumar Toro ta jihar Bauchi domin nuna fushinsu
  • Matasa sun fito zanga-zanga ne domin nuna adawa da kisan da wani mafarauci ya yi wa wasu mutum biyu da ke safarar gawayi
  • Fusatattun matasan sun ƙona gidaje tare da hana motoci wucewa ta garin bayan sun rufe hanyar da ta haɗa jihohin Plateau da Bauchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Wata mummunar zanga-zanga ta ɓarke a garin Zaranda Gari da ke ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi.

Zanga-zangar ta ɓarke ne a ranar Talata biyo bayan kashe wasu mutane biyu da wani mafarauci da ake kira Dandanga ya yi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari da asuba, sun kashe bayin Allah a Arewa

Zanga zanga ta barke a Bauchi
Matasa sun fito kan tituna a Bauchi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Matasa sun fito zanga-zanga a Bauchi

Jaridar The Punch ta rahoto cewa an harbe mutanen ne saboda safarar gawayi wanda hakan laifi ne bisa dokar da gwamnatin jihar ta kafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fusatattun matasa sun mayar da martani inda suka ƙona gidaje da dama da ke da alaƙa da jami’in tsaron tare da rufe hanyar gwamnatin tarayya da ta haɗa jihohin Bauchi da Plateau.

Zanga-zanga ta hana matafiya wucewa

Wani matafiyi mai suna Kabiru Danhajiya da ya maƙale a garin ya ce an ƙi bari motoci su wuce ta garin sakamakon zanga-zangar.

"Mun tarar an rufe hanyar tare da sanya wuta a bakin titi. Mutanen garin sun gaya mana cewa mafarauta sun cafke wasu mutum biyu ɗauke da gawayi sannan suka hallaka su."
"An gaya mana cewa mutanen garin suna neman sai gwamna ya zo domin ya shawo kan matsalar."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wani asibiti a Kaduna, sun tafka ɓarna

- Kabiru Danhajiya

Kabiru Danhajiya ya ƙara da cewa akwai ƴan sanda a wajen amma masu zanga-zangar sun fi su yawa sannan motoci sun maƙale sakamakon rufe hanyar da aka yi.

PDP ta faɗi masu ɗaukar nauyin zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta yi martani ga gwamnatin tarayya kan zanga zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a ƙasar nan.

PDP ta hannun sakataren ƴada labaranta na ƙasa ta ce abin kunya ne yadda gwamnatin tarayya ta kama yan Najeriya da suka fito zanga zangar tsadar rayuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng