Ambaliya: Dabbobin Dawa Masu Haɗari Sun Shiga Maiduguri, an Gargadi Jama’a

Ambaliya: Dabbobin Dawa Masu Haɗari Sun Shiga Maiduguri, an Gargadi Jama’a

  • Hukumar gidan dabbobi a Maiduguri ta fitar da sanarwa bayan ambaliya ta shiga gidan tare da tafiya da dabbobi masu yawan gaske
  • Babban manajan gidan dabbobin ya bayyana cewa a yanzu haka wasu dabbobi masu hadari da yawa sun shiga cikin al'umma
  • Manajan mai suna Ali Abatcha Don ya ce ambaliyar ta jawo asarar dabbobi masu yawan gaske yayin da wasu kuma ba a gansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Ana cigaba da lissafa barna da ambaliyar ruwa ta jawo a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A yanzu haka rahoto ya nuna cewa ambaliyar ta shiga gidan ajiye dabbobina Maiduguri inda ruwa ya kwaso dabbobi cikin jama'a.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta fadi yadda za ta raba yan Najeriya miliyan 100 da talauci

Ambaliya
Ambaliya ta kashe dabbobi a Maiduguri. Hoto: Adamu Bulama
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa hukumar gidan dabbobin ta yi gargadi kan kaucewa shiga ruwa domin tsoron cin karo da dabbobin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dabbobi sun shiga Maiduguri ana ambaliya

The Cable ta wallafa cewa manajan gidan dabbobin jihar Borno, Ali Abatcha Don ya ce dabbobi kamar macizai da kada sun shiga cikin gari.

A karkashin haka, Ali Abatcha Don ya yi kira ga al'umma kan yin taka tsantsan domin kaucewa hadarin dabbobin.

Ambaliya ta kashe dabbobi a Maiduguri

Haka zalika, Ali Abatcha Don ya tabbatar da cewa ambaliyar ta jawo mummunar asara a gidan dabbobin.

A lokacin tattara wannan rahoton, manajan ya bayyana cewa kashi 80% na dabbobin gidan sun mutu a sanadiyyar ambaliyar.

Kokarin kare sauran dabbobi a Maiduguri

Ali Don ya ce a yanzu haka suna ƙoƙarin ganin sun tabbatar da cewa sauran dabbobin da suke wajensu ba su hallaka ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta yi bincike kan mutuwar mutane sama da 100 a Jigawa

A karshe, manajan ya yi kira na musamman ga al'ummar jihar da su cigaba da rokon Allah ya kawo musu sauki.

Ambaliya: Kwankwaso ya tura sakon jaje

A wani rahoton, kun ji cewa jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya jajantawa al'ummar Borno kan ambaliyar ruwa da ta mamaye sassan jihar.

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ya ga hotuna masu ban tsoro daga Maiduguri, inda ambaliyar ruwa ta mamaye wurare daban daban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng