Bayan Sako Shugaban NLC, Hukumar DSS Ta Bayyana Dalilin Kai Samame Ofishin SERAP
- Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da kai ziyara ofishin kare hakkin jama’a da tattalin arziki (SERAP) da ke Abuja a ranar Litinin
- Yayin da take watsi da zarge-zargen cin zarafi da karya doka, DSS ta ce jami'anta sun ziyarci ofishin SERAP domin gudanar da bincike
- Martanin da DSS ta yi na zuwa ne awanni kadan bayan da hukumar ta sako shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da ta kama jiya Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da kai 'ziyara' ofishin kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa (SERAP) da ke Abuja.
Kungiyar SERAP ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya umarci hukumar DSS da ta kawo karshen cin zarafi da keta 'yancin ‘yan Najeriya da aka yi mata.
"Ba mu saba doka ba" - DSS
A ranar Talata, jaridar Daily Trust ta ruwaito DSS ta kalubalanci kalaman SERAP, inda ta ce ba ta karya wata doka ba a ziyarar da ta kai ofishin kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar DSS ta ce babu wani jami’in hukumar da ke dauke da makami lokacin da suka ziyarci ofishin SERAP domin gudanar da bincike akai-akai.
“Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta samu korafe korafe game da zargin mamaye ofisoshin SERAP da ke Abuja da Legas ba bisa ka’ida ba.”
“Wannan korafin ba gaskiya ba ne kuma an kirkire shi domin karkatar da tunanin jama'a.
- A cewar DSS.
Dalilin DSS na ziyartar SERAP
Sanarwar ta bayyana cewa wasu tawagar jami'an DSS biyu ne suka ziyarci ofishin SERAP domin gudanar da bincike, kuma ba sa dauke da makamai, inji rahoton Channels TV.
“Hukumar na ci gaba da bayyana cewa irin wannan bincike abu ne da aka saba kuma babu ta hanyar da yin hakan ya sabawa doka ko kuma abin da za a kira mamaya.
“Saboda haka, hukumar ta DSS ta na kira ga jama’a da su yi watsi da wadannan labaran karyar, domin ta na kan kudirinta na yin amfani da kwarewa wajen gudanar da aikinta.”
- A cewar sanarwar.
DSS ta sako shugaban NLC
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar DSS ta bada belin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Kwamred Joe Ajaero, da misalin karfe 11:25 na dare.
Jami'an DSS sun cafke Ajaero da safiyar ranar Litinin a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe, Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng